Yadda shugaba Buhari ya kamata ya gudanar da sharia'ar Diezani - Stella Oduah

Yadda shugaba Buhari ya kamata ya gudanar da sharia'ar Diezani - Stella Oduah

- Sanata Stella Oduah ta sharwarci gwamnatin shugaba Buhari akan hanyar da ya kamata tabi wajen shari'ar Diezani

- Senatan mai wakiltan Anambra tayi kira da gwamnatin shugaba Buhari da tabi hanyoyin da dokar kasa ta shimfida wajen gudanar da shari'ar

Yar majalisar dattawa, Sanata Stella Oduah tayi kira ga gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari da su bi hanyoyin da doka ta shimfida wajen bincike da gudanar da shariah tsohuwar badakallar kudi na ministan man fetur Allison Diezani Madueke.

A ranar Talata, 12 ga watan Satumba, tsohuwar ministan jiragen saman Oduah ta bayyana wa manema labarai a Abuja cewa ya kamata a gurfanar da Allison Madueke a gaban kotu, idan kotu ta tabbatar da laifin ta sannan sai a fara kwace kayayyakin ta.

Yadda shugaba Buhari ya kamata ya gudanar da sharia'ar Diezani - Stella Oduah

Yadda shugaba Buhari ya kamata ya gudanar da sharia'ar Diezani - Stella Oduah

"Muna da dokoki a kasar nan, muna da hanyoyin da ake bi wajen gudanar da shariah, idan dai muna biyaya ga doka da oda toh ya kamata mu gudanar da duk abin da zamuyi kamar yadda doka ta tanada.

DUBA WANNAN: Gwamna Ikpeazu ya sanya dokar hana fita a Aba yayin da sojoji suka dira a garin

''A fahimta ta, duk wani abu da akayi akasin yadda doka ta tanada, ya zama laifi shi kansa.''

A kwanakin baya NAIJ.com ta kawo muku rahoton yadda hukumar EFCC karkashin jagorancin Ibrahim Magu a ranar Alhamis, 7 ga watan Satumba tace sunyi nasarar karbo kashi 15 cikin 100 ne kawai na kudin da tsohuwar ministan man fetur din tayi awon gaba dashi.

Magu yace a halin yanzu, hukumar EFCC tana aiki tare da gwamnatin kasar Ingila domin dawo da Diezani gida Najeriya inda za'a gurfanar da ita gaban kotu domin zartar da sharaiah.

Shugaban rikon kwaryar na EFCC yace hukumar zatayi iya kokarinta ta karbo duk dukiyar Najeriya a hannun wanda suka sace.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kana kana da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.naij.com

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Badakalar Maina: Yadda aka raba gidaje 222 da Maina ya kwato

Badakalar Maina: Yadda aka raba gidaje 222 da Maina ya kwato

Badakalar Maina: Yadda aka raba gidaje 222 da Maina ya kwato
NAIJ.com
Mailfire view pixel