Hukumar soji ta musanta rahoton yin karon batta tsakanin ta da 'yan jarida a Umuahia ta jihar Abia

Hukumar soji ta musanta rahoton yin karon batta tsakanin ta da 'yan jarida a Umuahia ta jihar Abia

Sojoji sun dira a yankin na kudu maso gabas ne domin kwantar da tarzomar da masu son kafa kasar Biafra ke barazanar tayar wa.

Hukumar soji ta kasa ta bakin mataimakin jami'in hulda da jam'a, Major Oyegoke Badamosi, ta karyata labarin da ke yawo a kafafen sada zumunta na yanar gizo cewar sun yi karon batta tare da yin rotse ga wasu 'yan jarida a Umuahian jihar Abia.

Hukumar soji ta musanta karon batta tsakanin ta da 'yan jarida a Umuahia ta jihar Abia

Hukumar soji ta musanta karon batta tsakanin ta da 'yan jarida a Umuahia ta jihar Abia

Hukumar sojin ta tabbatar da samun sa-in-sa tsakanin ta da 'yan jaridar amma ba ta kai zuzutawar da ake wa batun a labaran da ake yadewa ba. Hukumar ta ce "a yayin da jami'an mu ke wucewa ta gaban ofishin kungiyar 'yan jaridun sai mu ka ga wasu daga cikin su na daukan hoton mu na bidiyo a wayoyi da na'urar daukan hoto, jami'an mu sun tsaya tare da kwace da lalata na'urorin da wayoyi da suka hada da; wayar iPad guda 1 da wasu wayoyi guda 2 kuma tuni kwamandan mu na runduna ta 82 yayi sulhu tsakanin yan jaridar da jami'an sojin".

DUBA WANNAN: Duk da kasancewar sa minista har yanzu bai daina zuwa teburin mai shayi karya kumallo ba: Hotuna da bidiyo

Hukumar sojin ta ce a shirye ta ke ta yi hukunci ga duk jami'in ta da ya nuna rashin da'a yayin gabatar da aikin sa tare da yin kira ga jama'a da su guji yada karya da jita-jita.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.naij.com

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gwamnatin Kano tana kashe naira biliyan 9 wajen biyan albashi a kowace wata

Gwamnatin Kano tana kashe naira biliyan 9 wajen biyan albashi a kowace wata

Gwamnatin Kano tana kashe naira biliyan 9 wajen biyan albashi a kowace wata
NAIJ.com
Mailfire view pixel