NLC ta yi alkawarin tona asirin gwamnonni da sukayi almundahana da kudin Paris Club

NLC ta yi alkawarin tona asirin gwamnonni da sukayi almundahana da kudin Paris Club

- Mun roki shugaban kasa da kada ya kara tura wa gwamnoni kudi har sai sun bayyana yadda suka yi amfani da na da

- A yanzu haka ma'aikatan gwamnatin jihar Zamfara sun tafi yajin aiki - Ayuba Wabba

- Abun farincki shine shugaban kasa yasan abun da ke faruwa a jihohi kuma yasan gwamnoni da suka ki biyan albashi

Kungiyan kwadagon na Najeriya (NLC) A ranar Talata tayi alkawarin tona asirin gwamnonin da suka ki amfani da kudaden Paris Club yadda yakamata.

Shugaban NLC, kwamared Ayuba Wabba yace har yanzu ma’aikata suna bin gwamnoni albashi duk da kudaden da aka kara ba su.

Wabba yace shugaban kasa Muhammadu Buhari yayi na’am da wasikar da kungiyan ta tura masa inda suka roki shi da kada ya kara tura wa gwamnoni sauran kudaden Paris Club har sai sun bayyana yadda suka yi amfani da na baya.

NLC ta yi alkawarin tona asirin gwamnonni da sukayi almundahana da kudin Paris Club

NLC ta yi alkawarin tona asirin gwamnonni da sukayi almundahana da kudin Paris Club

“Wasikar da muka rubuta wa shugaban kasa, yasa yayi maganar biyar albashi a taron mu na WCW, Inda muka roke shi da ka da ya kara sakar ma gwamnoni Kudin Paris Club dan basu cika alkawarin da suka yi ba.

KU KARANTA : Biyafara : Fani Kayode yayi Magana da Nnamdi Kanu a lokacin da sojoji su ka mamaye gidan sa

“Idan aka tuna baya ciyaman din Gwamnonin Najeriya ya tabbatar mana cewa zasu yi amfani da kudaden ne wajen kawo karshen matsalolin albashi da yan fensho. Amma abun takaice shi ne ba ayi hakan ba.

“A yanzu da na ke muku magana ma’aikatan gwamnatin jihar Zamfara sun tafi yajin aiki. Shi gwamnan Zamfara da yayi wannan maganar a madadin sauran gwamnonin ya kasa cika alkawarin da ya dauka. Wannan ya nuna irin yaudarar dake cikin gwamnati. Wannan shine dalilin da yasa muka rubuta wa shugabankasa wasika dan daukar mataki saboda ya nuna mana daban yake da gwamnoni.

“Akwai wasu jihohi da suka yi amfani da nasu kason yadda yakamata, amma jihohi kamar Ekiti, Kogi, Benue, da Zamfara sunki yin abun da yakamata da kudaden da yashiga hanun su.

“Kuma inda aka tuna abun da yafaru a majalisar dokoki na jihar Kogi, wani dan majalisar ya nemi a bayyana masa yadda aka yi amfani kudin Parsi Club da aka ba jihar, rikici ya barke har aka fasa ma kai kuma wannan yayi sanadiyar tsige kakakin majalisar Jihar. Wannan ya nuna yadda abubuwa suka tabarbare a jihohi.

“Amma abun farinciki anan shine Shugaban kasa ya san abubuwan dake faruwa a jihohi, kuma ya san gwamnonin da basu yi amfani da kudaden yadda yakamata ba, kuma ya fara musu magana."

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.naij.com

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gwamnatin Kano za ta tallafa wa hukumar FRSC don rage haɗura a hanyoyi

Gwamnatin Kano za ta tallafa wa hukumar FRSC don rage haɗura a hanyoyi

Gwamnatin Kano za ta tallafa wa hukumar FRSC don rage haɗura a hanyoyi
NAIJ.com
Mailfire view pixel