Budar Aiki: Shugaba Buhari zai kai ziyara jihar Kano

Budar Aiki: Shugaba Buhari zai kai ziyara jihar Kano

NAIJ.com ta kawo muku labarin ziyarar da shugaban Kasa Muhammadu Buhari yake daf da kai wa jihar Kano, sanadiyar bude sababbin asibitoci da aka kammala gininsu da kuma zuba musu kayan aiki na gani na fade.

An kiyasta cewa, da zarar an bude wannan asibitoci, jihar Kano za tayi fice wajen kere kowace jiha a fadin kasar nan, ta fuskar asibiti mai zubi irin na kasashen da suka ci gaba.

Gwamnan Jihar Kano Dr Abdullahi Umar Ganduje ne ya bayyana hakan, yayin ziyarar duba aikin sanya kayayyakin asibitin unguwar Giginyu da kuma asibin yara wanda ke daura da hanyar gidan Zoo.

Rahotanni sun bayyana cewa, gwamnatin jihar Kano ta kammala wannan asibitoci biyun tare da sayan kayayyakinsu kan kudi kimanin naira biliyan uku.

Ganduje wajen duba kayan aiki a daya daga cikin asibitocin

Ganduje wajen duba kayan aiki a daya daga cikin asibitocin

An fara gini wannan asibitoci tun shekaru goma da suka gabata, wanda gwamna Ganduje ya yi alkawarin ci gaba da duk ayyukan da gwamnatocin baya suka bari, don a cewarsa hakan zai kawowa jihar ci gaba.

Na'urori a asibitin

Na'urori a asibitin

A jawabinsa, Gwamnan ya nuna jin dadinsa ga yadda aikin yake tafiya a cikin Asibitocin guda biyu. Inda ya kara kira ga 'yan kwangilar da su ci gaba da aiki babu dare ba rana don ganin aikin ya kammala.

Na'ura mai gani har hanji

Na'ura mai gani har hanji

Wasu daga cikin kayan aiki da aka sanya a asibitocin sun hadar da; na'ura mai gani har hanji wato MRI, wadda idan ban da asibitin Fadar Shugaban Kasa, babu ita a duk jihohin Najeriya, sai CT Scan, Mammography wanda ake cire kari na mama, da injinan wanke koda da sauran injina wadanda ake yayi a kasashen ketare da su ka cigaba ta fuskar zamananci, kimiyya da kuma fasaha.

KU KARANTA: Yanzu Yanzu: Jami’an tsaro sun mamaye jihar Rivers bayan karo da akayi tsakanin sojoji da yan kungiyar IPOB

Karin hotuna na asibitin:

Sashen asibitin yara daura da hanyar gidan Zoo

Sashen asibitin yara daura da hanyar gidan Zoo

Ganduje wajen duba aikace-aikace

Ganduje wajen duba aikace-aikace

Na'ura ta CT Scan

Na'ura ta CT Scan

Ganduje tare da mataimakin sa Farfesa Hafiz wajen duba aikin

Ganduje tare da mataimakin sa Farfesa Hafiz wajen duba aikin

Domin shawara ko bamu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.naij.com

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Taran aradu da ka: wata Hajiya ta dauki gabaran biya ma Mijinta sadaki don ya yo mata kishiya

Taran aradu da ka: wata Hajiya ta dauki gabaran biya ma Mijinta sadaki don ya yo mata kishiya

Bambarakwai: Uwargida zata biya ma Maigida sadaki don ya kara aure (Hotuna)
NAIJ.com
Mailfire view pixel