Ka daina nuna kwaɗayinka a fili, ba haka ake zama shugaban ƙasa ba – Gwamna Kashim ga Atiku

Ka daina nuna kwaɗayinka a fili, ba haka ake zama shugaban ƙasa ba – Gwamna Kashim ga Atiku

Gwamnan jihar Borno Kashim Shettima ya shawarci tsohon mataimakin shugaban kasa Alhaji Atiku Abubakar daya daina gogoriyon zaman shugaban kasar Najeriya, tun da zafin nema baya kawo samu.

Gwamnan ya fada ma Atiku cewa tarihi ya nuna babu wani wanda ya zama shugaban kasa Najeriya saboda zafin neman sa, tun daga shekarar 1979, inda yace duk mutanen da suka shugabanci Najeriya daga wannan lokaci, ba nema suka yi ba, mulkin ne ya neme su.

KU KARANTA: Wasu hotunan fitaccen malamin addinin Musulunci, Sheikh Abubakar Gumi a zamanin rayuwarsa

“Shehu Sahagari na zaman zaman shi aka bukaci yayi takarar shugaban kasa a shekarar 1979, Obasanjo kuwa daga kurkuku ma aka dauko shi ya tsaya takara ba tare da ya nema ba. duk a irin shahararrun mutanen dake neman takarar shugaban kasa a 2007, amma aka dauko gwamnan jihar Katsi, Umar Yar’adua aka bashi mulki.

Ka daina nuna kwaɗayinka a fili, ba haka ake zama shugaban ƙasa ba – Gwamna Kashim ga Atiku

Gwamna Kashim da Atiku

“Ka duba kauna da soyayya da jama’a ke nuna ma shugaban kasa Muhammadu Buhari, ko shi bai ci zabe ba a takara da yayi sau uku, har sai lokacin daya yanke shawarar ba zai sake tsayawa takara ba, yayi ritaya daga siyasa, sai ga shi an roko shi a 2015, kuma ya zama.” Inji Kashim.

Ba wai ina cewa jama’a basu da ikon neman mukaman mulki bane, ko kuma wai hakan ba zia zamo da mai ido ga kasar bane, a’a. manufata itace bai dace mu dinga yin shakulatin bangaro da tarihi ba, kamar yadda NAIJ.com ta ruwaito shi yana fadi.

“Ko wadanda ma suka zama mataimakan shugaban kasa, su kansu ba nema suka yi ba, mukaman ne suka neme su, ka duba Alex Ekweme, yana zamansa aka ce yazo ya zama mataimakin Shagari a 1979, shi kansa Atiku takarar gwamna yaci a Adamawa, amma aka gayyato shi ya zama mataimakin Obasanjo, Kamar yadda shima Jonathan bai nema ba, amma aka bashi mataimakin Yar’adua. Haka zalika Osinbajo.”

Don haka ya dace mu dinga waiwaye, don gano bakin zaren, kuma idan ma ana maganan sake tsayawa takarar zabe ne, tarihi ya nuna in banda Jonathan, babu wanda ya sake tsayawa neman tazarce ya fadi, don haka tarihi ya nuna idan Buhari ya tsaya takara, za ci.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.naij.com

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gwamna Ganduje ya koka game da naira biliyan 9 da gwamnatinsa ke kashewa wajen biyan albashi a kowane wata

Gwamna Ganduje ya koka game da naira biliyan 9 da gwamnatinsa ke kashewa wajen biyan albashi a kowane wata

Gwamnatin Kano tana kashe naira biliyan 9 wajen biyan albashi a kowace wata
NAIJ.com
Mailfire view pixel