Jihar Kano ta dauki aniyyar yakar fataucin miyagun kwayoyi

Jihar Kano ta dauki aniyyar yakar fataucin miyagun kwayoyi

Gwamnatin jihar Kano ta sha alwashin kafa kwamitin masu yaki da fataucin miyagun kwayoyi domin tallafawa hukumar yaki da miyagun kwayoyi (NDLEA) wajen ci gaba da yakin ta akan safara da kuma fataucin miyagun kwayoyi a jihar

Shugaban cibiyar korafe-korafe da kuma yakar cin hanci da rashawa na jihar Alhaji Muhuyi Rimin-Gado, ya bayyana hakan yayin ganawa da kwamanda na hukumar NDLEA, Hamza Umar a ofishinsa.

Rimin-Gado ya ce kwamitin zai hada gwiwa da ma'aikatan hukumar NDLEA da sauran jami'an tsaro don magance shaye-shayen miyagun kwayoyi da ya kamari a jihar musamman ma matasan jihar.

Gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje

Gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje

Ya ce, wannan yunkuri na gwamnatin jihar ya zo domin tallafawa da kuma nuna goyan baya akan kokarin da gwamnatin tarayya take wajen yakin fataucin miyagun kwayoyi a kasar nan.

KU KARANTA: APC za tayi zaman tattaunawa akan Aisha Alhassan da Atiku

Ya kara da cewa, kwamitin da gwamnatin za ta kafa, za suyi aiki ne karkashin kulawar hukumar NDLEA tare da hadin gwiwa na ministiri ta kananan hukumomin jihar.

A na shi bangaren, Hamza Umar ya nuna farin cikin sa da kuma godiya, sannan ya baiwa gwamnatin jihar goyon baya akan wannan yunkuri na yakar fataucin miyagun kwayoyi.

Domin shawara ko bamu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.naij.com

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gwamna Ganduje ya koka game da naira biliyan 9 da gwamnatinsa ke kashewa wajen biyan albashi a kowane wata

Gwamna Ganduje ya koka game da naira biliyan 9 da gwamnatinsa ke kashewa wajen biyan albashi a kowane wata

Gwamnatin Kano tana kashe naira biliyan 9 wajen biyan albashi a kowace wata
NAIJ.com
Mailfire view pixel