Rikicin Biafra: 'Yan kungiyan IPOB sun kai hari unguwar hausawa a jihar Ribas

Rikicin Biafra: 'Yan kungiyan IPOB sun kai hari unguwar hausawa a jihar Ribas

- Rahotanni sunce 'yan kungiyar IPOB sun kai hari unguwar Hausawa da ke Ribas

- An kone wasu daga cikin kayayyakin hausawan

- An kone wani masallaci kurmus a harin da aka kai

An sami rahotanni cewa 'yan kungiyar fafutikan kafa kasar Biafra IPOB sun afka wa wani unguwar Hausawa mai suna Oyigbo a jihar Ribas. Kamar yadda rahoton yace, an kai harin na a ranar Talata, 12 ga wata Satumban wannan shekaran.

Daga bisani, suma Hausawan mazauna unguwar sun kai wata harin domin rama abinda akayi musu.

Rikicin Biafra: 'Yan kungiyan IPOB sun kai hari unguwar hausawa a jihar Ribas

Rikicin Biafra: 'Yan kungiyan IPOB sun kai hari unguwar hausawa a jihar Ribas

Wani rahoton kuma yace yan kungiyar IPOB din sunyi artabu ne da sojoji a unguwar, an kone kayayakin mutane har ma da masallaci.

DUBA WANNAN: Gwamna Ikpeazu ya sanya dokar hana fita a Aba yayin da sojoji suka dira a garin

A halin yanzu dai, Gwamna Okezie Ikpeazu na jihar Abia ya saka dokar hana fita a garin na kwana 3 domin kare afkuwar wani rikicin tsakanin al'ummar garin da rundunar soji.

NAIJ.com ta bada rahoton cewa rundunar soji sun fara gudanar da wata shiri na tabattar da zaman lafiya da sukayi wa lakabi da 'Rawan Kumurci' amma yan kungiyar IPOB din basu ji dadin hakan ba.

Kungiyar IPOB din tayi ikirarin cewa sojoji sunyi wa gidan Nnamdi Kanu kawanya amma rundunar sojin ta musanta wannan zargin, sunce wucewa kawai sukayi ta gaban gidan.

Jaridar Vanguard ta bada wani rahoto ranar Talata inda gwamnan jihar Abia yace yayi ammana da matakin da gwamnatin tarayya ta dauka domin samar da zaman lafiya amma yayi kira ga sojin suyi aikinsu yadda doka ya tanadar.

Yace dokar hana fitar zata fara aiki ne daga karfe 6 na yamma zuwa 6 na safe daga ranar Talata zuwa ranar Alhamis.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kana kana da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.naij.com

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gwamna Ganduje ya koka game da naira biliyan 9 da gwamnatinsa ke kashewa wajen biyan albashi a kowane wata

Gwamna Ganduje ya koka game da naira biliyan 9 da gwamnatinsa ke kashewa wajen biyan albashi a kowane wata

Gwamnatin Kano tana kashe naira biliyan 9 wajen biyan albashi a kowace wata
NAIJ.com
Mailfire view pixel