Bayafra: Dalilin da yasa Buhari ya aiko soji suyi min kisan gila - Nnamdi Kanu

Bayafra: Dalilin da yasa Buhari ya aiko soji suyi min kisan gila - Nnamdi Kanu

- Kungiyar IPOB tayi ikirarin cewa shugaba Buhari ne ya aike sojoji domin su halaka Nnmadi Kanu domin ya jajirce wajen kwato hakin yan Biafra

- Kungiyar tace zuwan sojin yankin kudu maso gabashin Najeriya ya haifar da tashin hankali

- Daga karshe kungiyar tayi gargadi cewa idan har gwamnatin Buhari tayi nasarar kashe Kanu, fitinar da zata barke a Najeriya baza ta misaltu ba

Shugaban kugiyar IPOB, Nnamdi Kanu yayi ikirarin cewa shugaba Buhari ne ya aike da rundunar sojin Najeriya domin suyi wa gidansa 'kawanya.

A cewar Kanu, Buhari ya baiwa sojojin ''Hausa/Fulani'' umarnin suyi min kisan gila domin na sadaukar da rayuwata wajen kwato hakin mutanen Bayafra.

A sakon da ya aike wa Daily Post ta hannun mai magana da yawun kungiyar ta IPOB, Emma Powerful, Kanu yayi ikirarin cewa rundunar sojin Najeriya sunyi shiri tsaf domin su kashe shi, shiyasa suka fada wa tawagar sa a mahadar Ubakala a hanyar sa ta zuwa aiki.

Bayafra: Dalilin da yasa Buhari ya aiko soji suyi min kisan gila - Nnamdi Kanu

Bayafra: Dalilin da yasa Buhari ya aiko soji suyi min kisan gila - Nnamdi Kanu

Ga dai sakon kamar haka: ''Mu yan kungiyar IPOB a karkashin shugabancin Mazi Nnamdi Kanu jagoran gidan radiyo da talabijin na Biafra muna so mu jawo hankalin mutanen Najeriya har ma da duniya baki daya da su sani cewa shugaba Buhari da sojojin sa yan hausa fulani masu kokarin tabbatar da jihadi sun mamaye gidan Nnamdi Kanu da ke Afarauku Ibeku a garin Umuahia da ke jihar Abia.

DUBA WANNAN: Tirkashi!: Za'a tura shi kurkuku saboda ya koyar da addinin Musulunci a kasar China

"A halin yanzu babu kwanciyan hankali a garin Umuahia. Babban kotun tarayya ta hada baki da gwamnatin tarayya a karkashin shugabancin Manjo Janar Buhari sun kun karbe paspo din Nnamdi Kanu, sun hana shi fita daga kasan domin suna so su halaka shi a Najeriya. Kisan gilar da akeyi ma faran hula yan Bayafra da niyyar kashe Kanu da gwamnati ke dashi abu ne da ya kamata yan Biafra su ki amince wa dashi."

Har ila yau, sanarwan ta cigaba da cewa zagayen da sojoji keyi a garin Umuahia da sukayi wa lakabi da 'Rawan kumurci" kashi na 2 ya rikita yankin Kudu maso gabashin kasan.

Daga karshe sanarwan tace duk wani yunkiri na kashe shugaban IPOB Nnamdi Kanu zai haifar da mumunar fitina a Najeriya idan har akayi nasarar hakan.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kana kana da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.naij.com

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gwamna Ganduje ya koka game da naira biliyan 9 da gwamnatinsa ke kashewa wajen biyan albashi a kowane wata

Gwamna Ganduje ya koka game da naira biliyan 9 da gwamnatinsa ke kashewa wajen biyan albashi a kowane wata

Gwamnatin Kano tana kashe naira biliyan 9 wajen biyan albashi a kowace wata
NAIJ.com
Mailfire view pixel