Gwamna Ikpeazu ya sanya dokar hana fita a Aba yayin da sojoji suka dira a garin

Gwamna Ikpeazu ya sanya dokar hana fita a Aba yayin da sojoji suka dira a garin

- Gwamna Ikpeazu ya sanya dokar hana fita a Aba yayin da sojoji suka afkama garin

- Dokar ta fara a yau, daga 6 na yamma zuwa 6 na safe daga ranar Talata zuwa Alhamis

- Dokan zai kawar da salwanta rayuka da dukiyoyin mutane yayin da sojoji ke gudanar da ayyukan su

Gwamnan Jihar Abia Dakta Okezie Ikpeazu ya sanya dokar hana fita a garin Aba, wanda gari ne na kasuwanci a sakamakon afkawa garin da sojoji suka yi.

A bayanai da gwamnatin jihar ta fitar, gwamnan ya nuna damuwarsa kan gudanar da aiki da sojoji suka yi mai taken ''Rawar Kumurci'' karo na biyu a nan jihar da wasu jihohin kudu maso gabas. Dokar tana farawa ne daga 6 na yamma zuwa 6 a safe daga ranar Talata zuwa ranar Alhamis.

A 'yan sa'o'i dakan da suka wuce ne rahotanni da bidiyo ya nuna rundunar sojoji sun mamaye gidan shugaban kungiyar IPOB, Mazi Nmamdi Kanu a yayin da su kuma matasa 'yan kungiyar suka katange hanyar da ya isa zuwa gidan.

Gwamna Ikpeazu ya saka dokar kulle a garin Aba bayan sojoji sun dira jihar

Gwamna Ikpeazu ya saka dokar kulle a garin Aba bayan sojoji sun dira jihar

A 'yan kwanakin baya ne kuma rundunar sojojin suka afkawa jihohin Kudu maso Gabas da makamai da nufin magance matsaloli na garkuwa da mutane da hatsaniyar gwagwarmaya don tabbatar da hadin kan kasan nan.

DUBA WANNAN: Tirkashi!: Za'a tura shi kurkuku saboda ya koyar da addinin Musulunci a kasar China

Sai dai Jihar Abia, Jihar da Nmandi Kanu yake, tana cikin firgici sakamakon artabun da matasa magoya bayan IPOB suka yi da rundunar sojoji a ranar lahadi a lokacin da sojojin suka afkawa gidan Kanu wai har suka kashe wasu daga cikin matasan.

Wutan al'amarin ya kara ruruwa ne a lokacin da wani bidiyo ya nuna sojoji suna kai komo a fusace a yankin gidan Kanu da motocin yaki wanda rundunar sojoji ta kira wannan salon aiki ''nuna karfin iko'' a Jihar.

Gwamnatin Jihar Abiya don kawar da wani hatsaniya da ka iya tasowa sakamakon wadannan al'a mura sai tayi gaggawan sanya dokan hana fita. Ta yi hakan ne don kare salwantar rayuka da dukiyoyin mutane. Kuma hakan zai ba rundunar sojojin gudanar da ayyukan su ba tare da samun wani cikas ba.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kana kana da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.naij.com

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gwamnatin Kano tana kashe naira biliyan 9 wajen biyan albashi a kowace wata

Gwamnatin Kano tana kashe naira biliyan 9 wajen biyan albashi a kowace wata

Gwamnatin Kano tana kashe naira biliyan 9 wajen biyan albashi a kowace wata
NAIJ.com
Mailfire view pixel