Biyafara : Fani Kayode yayi Magana da Nnamdi Kanu a lokacin da sojoji su ka mamaye gidan sa

Biyafara : Fani Kayode yayi Magana da Nnamdi Kanu a lokacin da sojoji su ka mamaye gidan sa

- Aikin sojoji shine kare ran alumma ba kashe su ba

- Abun da ka faruwa abun bakin cikin ne da takaici

- Nayi magana da Nnamdi Kanu, kanwarsa da lauyan sa

Tsohon ministan sufurin jirgin sama, Femi Fani Kayode, ya rubuta a shafin sa na tuwita cewa yayi Magana da shugaban yan asalin Biyafara IPOB, wanda aka ce sojoji sun tsare shi a gidan sa.

Fani-Kayode ya gargadi shugaban kasa Muhammadu Buhari, da ya dakatar da sojojin sa, “kafin a kashe mutanen da basu yi wa kowa laifi ba”.

Ya rubuta shafinsa cewa: “Yanzun nan nayi Magana da Nnamdi Kanu,tare lauyan sa da kanwar sa. Wannan abun bakin ciki ne da takaice kuma ba za mu yarda ba.

Biyafara : Fani Kayode yayi Magana da Nnamdi Kanu a lokacin da sojoji su ka mamaye gidan sa

Biyafara : Fani Kayode yayi Magana da Nnamdi Kanu a lokacin da sojoji su ka mamaye gidan sa

“Rana na biyu kenan da aka saka al’umman garin cikin firgici da tsoro. Sojoji suna ta harbe- harbe a iska da kan gini.

KU KARANTA : Abin da gwamnatin Nijeriya ya kamata ta yi don kawo karshen yajin aikin ASUU - Bishof

“Ina kira da @MBuhari da ya hana sojojin sa kashe mutanen da basu yi wa koya laifi ba. Aikin soja shine kare al’ummar ba kashe su ba."

NAIJ.com ta samu rahoton cewa sojoji sun kai wa gidan Kanu hari a safiyar Alhamsi da misalin karfe 5.3am suka fara harbe harbe.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.naij.com

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gwamna Ganduje ya koka game da naira biliyan 9 da gwamnatinsa ke kashewa wajen biyan albashi a kowane wata

Gwamna Ganduje ya koka game da naira biliyan 9 da gwamnatinsa ke kashewa wajen biyan albashi a kowane wata

Gwamnatin Kano tana kashe naira biliyan 9 wajen biyan albashi a kowace wata
NAIJ.com
Mailfire view pixel