Kungiyar Kwadago reshen jihar Zamfara ta shiga yajin aiki

Kungiyar Kwadago reshen jihar Zamfara ta shiga yajin aiki

Kungiyar kwadago reshen jihar Zamfara ta fada yajin aiki gadan-gadan sanadiyar rashin cika alkawurra da kuma yarjejeniyar da kungiyar ta kulla da gwamnatin jihar.

Shafin jaridar DAILY TRUST ya ruwaito cewa, tun a baya kungiyar ta baiwa gwamnatin jihar gargadin kwanaki 21 akan ta kawo karshen kalubalen da ma'aikatan jihar ke fuskanta, in kuwa ba haka ba za ta dauki mataki.

Ciyaman na kungiyar Bashir Mafara, ya bayyana hakan yayin ganawa da manema labarai a babban birnin jihar na Gusau cewa, ma'akatan jihar za su shiga yajin aiki a tun daga karfe 12:00 na daren Litinin, kuma babu wani abu da zai canja musu ra'ayi face gwamnatin jihar ta biya musu bukatunsu.

Kungiyar Kwadago reshen jihar Zamfara ta shiga yajin aiki
Kungiyar Kwadago reshen jihar Zamfara ta shiga yajin aiki

Marafa ya ce, kungiyar ta yi iyaka hakurin ta duba da yadda al'amurran jihar ke tafiya, amma kawowa yanzu cikin shekaru biyu har yanzu gwamnati bata cika alkawurranta ba.

KU KARANTA: Kiwon Lafiya: Hanyoyi 4 na kauracewa warin baki

Ya ce, akwai dubunnan ma'aikatan jihar musamman na makarantun Firamare da na kananan hukumomi da gwamnatin ke biyansu Naira 8,000 a matsayin albashin su na wata, wanda wannan ya janyo jihar ta kere kowace jiha wajen biyan albashi mafi karanci a fadin kasar nan.

Ya kara da cewa, abin takaici ne a ce gwamnatin jihar tana biyan fansho na Naira 4,000 a kowane wata duba da yadda wahalhalu na rayuwa suka yi mutane katutu.

Marafa ya yi Allah wadai da gwamnatin jihar akan kin biyan sababbin ma'aikata 1,400 da ta dauka tun a shekarar 2014.

Domin shawara ko bamu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel