Dalilin da yasa manyan 'yan siyasa ke son Buhari ya tsaya takara a shekarar 2019 - Sanata Shehu Sani

Dalilin da yasa manyan 'yan siyasa ke son Buhari ya tsaya takara a shekarar 2019 - Sanata Shehu Sani

- Manyan yan siyasa suna ma Buhari kallon abinci

- Al'umma suna son Buhari ya tsaya takara saboda suna ganin sa a matsayin mutumin kirii wanda zai gyara kasar

- Shugaban kasa datijjo ne kuma yafi duka yan jam'iyya sa dade wa siyasa sabdoa haka ya fi kowa sanin abun da yakamata

Senata mai wakiltar mazabar Kaduna na tsakiya senata Shehu Sani yace manyan yan siyasa suna ganin Buhari a matsayin “abinci” shiyasa su ke son ya tsaya takara a zaben shekara 2019.

Sani ya rubuta a shafinsa na Facebook cewa, a loacin da al’ummar su ke kiran shugaban kasa ya tsaya takara tsakanin su da Allah, su kuma manyan yan siyasa suna hura masa wuta ya fito takara saboda, sun dauki shi a matsayin “Abinci”.

Ya kara da cewa: “Baba ne kadai zai yanke shawarar kara tsaya wa takara.Dattijo ne kuma yafi duka yan jam’iyyar sa dade wa a siyasa, saboda haka yafi kowa sanin abin da yakamata yayi."

Dalilin da yasa manyan 'yan siyasa ke son Buhari ya tsaya takara a shekarar 2019 - Sanata Shehu Sani

Dalilin da yasa manyan 'yan siyasa ke son Buhari ya tsaya takara a shekarar 2019 - Sanata Shehu Sani

“Har yanzu kasar tana bukatar sa, amma shi kadai zai iya yanke shawara. Manyan yasa sun fara hura masa wuta ya fito saboda suna mishi kallon abinci."

KU KARANTA :Asari Dokubo ya caccaki Buhari bayan Mama Taraba ta bayyana goyon bayan ta ga Atiku

“Baba kaman kwararren direba wanda yake kan tafiya mai nisa, kuma fasinjojinsa sun yaba da kwarewar tukinsa, shi kadai ne zai iya yanke shawarar ko ya cigaba da tafiyar ko ya tsaya, shugaba ne ke zabar kujera da wurin da zai zauna a cikin tarihin kasar sa.”

“Dalilin da yasa al’umma suke son Buhari yacigaba da mulki shine dalilin da yasa wasu manyan yan siyasa suke son baba ya kara tsayawa takara. Al'umma suna ganin sa a matsyin mutumin kirki wanda zai gyara kasar, suka kuma yan siyasa suna mishi kallon hanyar kare kujerar su."

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.naij.com

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Naira ta sha kasa yayin da babban bankin Najeriya ya malalo $288miliyan a kasuwar canji

Naira ta sha kasa yayin da babban bankin Najeriya ya malalo $288miliyan a kasuwar canji

Naira ta sha kasa yayin da babban bankin Najeriya ya malalo $288miliyan a kasuwar canji
NAIJ.com
Mailfire view pixel