An bude masana'antar abincin dabbobi da kyankyashe kaji mafi girma a Afrika a Jihar Kaduna

An bude masana'antar abincin dabbobi da kyankyashe kaji mafi girma a Afrika a Jihar Kaduna

- An kaddamar da masana'antar abincin dabbobi da kyankyashe kaji a Jihar Kaduna.

- Masana'antar ta fi kowanne girma a duk fadin Nahiyar Afirik

- Zata sarrafa ton 360,000 na abincin dabbobi a shekara. Zata kyankyashe 'yan tsaki miliyan 1.6 duk sati

Masana'antar zata horas da manoma don samun amfani mai yawa. Zata samar wa al'umma ayyukan yi. Hukumar labarai ta kasa, NAN, ta bada rahoton cewa a yau ne za'a kaddamar da masana'antar abincin dabbobi da kyankyashe kaji wanda kamfanin Olam gina.

Shugaban kamfanin, Vinod Mishra, ya ce kamfanin wanda aka gina shi akan dala miliyan 150 ya kunshi sana'anta abincin dabbobi da kyankyashe kaji da kuma kiwo. Mishra ya shaidawa NAN cewa kamfani zai sarrafa ton 180,000 na masara da ton 75,000 na waken suya don sana'anta ton 360,000 na abincin dabbobi a shekara.

Jihar Kaduna: Gwamna El-Rufai ya kadamar da masana'anta kyankyashe kaji mafi girma a Afirika

masana'anta kyankyashe kaji mafi girma a Afirika

DUBA WANNAN: Dalilan da yasa Jonathan ya kasa magance matsalar Boko Haram - Obasanjo

Za kuma a kyankyashe 'yan tsaki guda mliyan 1.6 a kowani sati. Akwai rumbu a haraban kamfanin da zai ajiye ton 50,000, a kwai makamanci sa a wajen kamfanin. Kamfanin za kuma ta horas da manoma don samun amfani mai yawa baya ga samar da ayyukan yi da zata yi.

NAN dai ta iya tuna cewan Gwamnan Jihar Kaduna, Nasiru El Rufa'i ya kaddamar da kafa wannan masana'anta ne a rananr 10 ga watan Afirilu, 2016, a kauyen Chikpiri Gabas.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kana kana da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.naij.com

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gwamna Ganduje ya koka game da naira biliyan 9 da gwamnatinsa ke kashewa wajen biyan albashi a kowane wata

Gwamna Ganduje ya koka game da naira biliyan 9 da gwamnatinsa ke kashewa wajen biyan albashi a kowane wata

Gwamnatin Kano tana kashe naira biliyan 9 wajen biyan albashi a kowace wata
NAIJ.com
Mailfire view pixel