Manoma a jihar Jigawa sun rungumi sana'ar noman dankali

Manoma a jihar Jigawa sun rungumi sana'ar noman dankali

- Noman dankalin hausa ya fara habaka a jihar Jigawa

- Manoma da yawa sun rungumi sana'ar noman dankali

- Rashin aikin yi ga samari ya sa da yawan su sun koma gona

Manoma a jihar Jigawa zasu fara noman dankalin hausa. A wannan shekarar manoma 5,000 ne suka shiga sana’ar noman dankalin hausa wanda tuni wasu jihohin sun dau shekara da shekaru suna noman dankalin hausa.

Duk da cewa ana noman dankalin hausa a arewacin Najeriya sosai, sai a ‘yan shekarun nan ne manoma a jihar suka fara noman dankali wanda suka ga mamaki a yadda noman ya karbu a gonar tasu.

A rashin sanin ilimin noman dankalin hausa ne wasu manoman suke ganin kasar su ba ta noman dankali bace musamman manoma daga garin Birnin Kudu. Sai bayan da mutane kadan suka fara noman suka ga ribar sannan wasu suka shiga harkar noman suma.

Manoma a jihar Jigawa sun rungumi sana'ar noman dankali
Manoma a jihar Jigawa sun rungumi sana'ar noman dankali

Noman dankalin ba karamar riba bace domin kuwa za a iya noma shi sau uku a shekara, hakan zai sa mutanen jihar su sami aikin yi ba sai sun tafi wasu garuruwa neman sana’a ba. Yanzu kaasuwar dankalin hausa ta bude yadda mutane suka gano wa cin shi har masu sayar da abinci a kan hanya

Mutane da yawa da suka kammala karatun digirin su sun shiga sana’ar noma, da farko manoman suna musu dariya ganin kasar su ba ta noma dankali bace, amma bayan watanni sai gashi noma ya habbaka.

DUBA WANNAN: Matasa sun kwace motar wanda ya yi hayar su bayan ya gaza biyan su hakkin su

Noman dankali kuwa daga bakin manoman sun ce baya bukatar kashe makudan kudi. A cikin wata hudu manoman ke girbe shukar su kuma su hada kyakyyawar riba. Cikin shekara guda kuwa zasu juya shukar har sau uku.

Amma babban kalubale da suke fuskanta shine beraye da barayin gona, amma da sun samu sun magance wannan matsaloli to kuwa noman dankali sauki gare shi da araha.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel