Hatsarin mota yayi sanadiyar mutuwar mutane 19 a Kano

Hatsarin mota yayi sanadiyar mutuwar mutane 19 a Kano

- Fasinjoji 18 sun kune kurmus a hadarin hanyar Kano

- 15 suna babban asibitin Bichi

-Hadarin ya auku ne yayin da motoci biyu cike da fasonjoji suke kokarin wuce juna

Hukumar kare hadura da manyan hanyoyi na kasa (FRSC) ta ce mutane 19 suka rasa rayukan su ta dalilin hadarin mota da aka yi akan hanyar Kano zuwa Katsina.

Mai Magana da yawun hukumar FRSC na Jihar Kano Kabir IbrahimDaura ya bayyana wa manema labarai akan aukuwan hatsarin a ranar Asabar.

Kabir-Daura ya ce lamarin ya faru ne kusa da Lambun Garban Bichi, a gefen garin Bichi, da misalin karfe 8:30 na safiyar ranar Jumma'a.

Hatsarin mota yayi sanadiyar mutuwar mutane 19 a Kano
Hatsarin mota yayi sanadiyar mutuwar mutane 19 a Kano

A jawabin sa yace, "al'amarin ya faru ne lokacin da wani motar bas Peugeot J5 da kuma karamar mota na Toyota C20 suka hade da juna lokacin da suke kokarin wuce juna."

KU KARANTA : Mama Taraba ta yi murabus idan tana son yin aiki da Atiku - Shehu Sani

"A take a wajen motocin suka kama da wuta, wanda yayi sanadiyar mutuwar fasinjoji 18 a cikin fasinjoji 34, duka motocin sun kune kurmus."

“Akwai fasinjoji 34 a cikin duka motocin, 18 sun kune kurmus a wajen, daya kuma ya cika a asibiti,” inji shi.

Kabir-Bichi yace sauran fasinjojin 15 suna babban asibitin Bichi karkashin kulawan likitoci.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel