Takarar shugaban ƙasa a 2019: Shehu Sani ya jinjina ma Buhari bisa ɓoye matakin da zai ɗauka dangane da takara karo na 2

Takarar shugaban ƙasa a 2019: Shehu Sani ya jinjina ma Buhari bisa ɓoye matakin da zai ɗauka dangane da takara karo na 2

Sanatan al’ummar Kaduna ta tsakiya Sanata Shehu Sani ya jinjina ma shugaban kasa Muhammadu Buhari dangane da danne bayyana takarar sa na shugaban kasa a shekarar 2019.

Shehu Sani ya bayyana haka ne a wata hira da yayi da Channels TV a ranar Juma’a 8 ga watan Satumba inda yace duk shawarar da Buhari ya yanke a yanzu zai shafi tsarin gudanar da mulki.

KU KARANTA: Ramuwar gayya: Makiyaya sun kashe mutane 20 a ƙauyen jihar Filato

Majiyar NAIJ.com ta ruwaito Sanatan yana fadin “Idan ya bayyana burinsa na yin takara, wannan mataki zai kashe ma jama’a da dama damarsu na tsayawa takara."

Takarar shugaban ƙasa a 2019: Shehu Sani ya jinjina ma Buhari bisa ɓoye matakin da zai ɗauka dangane da takara karo na 2

Shehu Sani

Shehu Sani ya kara da cewa “Idan kuma yace ba zai yi takara ba, hakan zai kawo karshen ayyuakan gudanar mulki a kasar nan, don kowa zai fara gogoriyon takarar 2019.”

Daga karshe Shehu Sani yace bayan nazari mai tsawo ya gao cewa matakin da shugaban kasa Muhamamdu Buhari ya yanke na kin bayyana matsayinsa dangane da takara a 2019 yayi daidai.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.naij.com

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Naira ta sha kasa yayin da babban bankin Najeriya ya malalo $288miliyan a kasuwar canji

Naira ta sha kasa yayin da babban bankin Najeriya ya malalo $288miliyan a kasuwar canji

Naira ta sha kasa yayin da babban bankin Najeriya ya malalo $288miliyan a kasuwar canji
NAIJ.com
Mailfire view pixel