Da zafi zafi: Gwamnati ta shiga wata ganawar sirri da ASUU

Da zafi zafi: Gwamnati ta shiga wata ganawar sirri da ASUU

Yanzun nan tawagar gwamnatin tarayya da bangaren kungiyar Malaman jami’a, ASUU sun shiga zaman tattaunawa don kokarin kawo karshen yajin aikin da suka shiga, inji jaridar Premium Times.

A wannan zama na uku ne ake sa ran za’a kawo karshen yajin aikin, ministan kwadago, Chris Ngige yace gwamnati ta shirya zaman ne don ganin ta biya ma Malaman bukatunsu don su koma bakin aiki.

KU KARANTA: An tasa ƙeyar wani Direba gaban Alkali kan casa wani Ɗansanda da yayi a bakin aiki

“Mun kira wannan zama ne don karkare batutuwan da suka janyo yajin aikin” Inji Ngige.

Majiyar NAIJ.com ta ruwaito ministan yana fadin za’a tattauna batutuwan da suka shafi zancen alawu alawus da malaman ke bi, da kuma batun zuba makudan kudi a jami’an Najeriya don ciyar dasu gaba.

Da zafi zafi: Gwamnati ta shiga wata ganawar sirri da ASUU

Shuwagabannin ASUU

Ministan Ilimi, Malam Adamu Adamu yace bangarorin biyu zasu cigaba da tattauanawa don gano bakin zaren, tare da tabbatar da an bude jami’o’in.

Shima shugaban ASUU, Biodun Ogunyemi yace da zarar an kammala tattauna matsalolin, kuma aka gano bakin zaren, zasu koma ga shuwagabannin kungiyar, don daukan mataki.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.naij.com

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gangamin PDP: Nyesom Wike da Uche Secondus sun kai wa Bode George ziyara a gidan sa

Gangamin PDP: Nyesom Wike da Uche Secondus sun kai wa Bode George ziyara a gidan sa

Gangamin PDP: Nyesom Wike da Uche Secondus sun kai wa Bode George ziyara a gidan sa
NAIJ.com
Mailfire view pixel