Tonon silili: Asirin wata Sanatan Najeriya data sayi gidan naira miliyan 540 a Landan ya tonu

Tonon silili: Asirin wata Sanatan Najeriya data sayi gidan naira miliyan 540 a Landan ya tonu

An binciko yadda wata tsohuwar minista a gwamnatin tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan Stella Oduah tayi bindiga da kudin al’umma wajen siyan wani katafaren gida a birnin Landan, Inji Sahara Reporters.

Ita dai wannan tsohuwar minista, wanda a yanzu take Sanata tayi amfani da sunan wani kamfani ne (ADRIATIC LAND 4 LIMITED ) wajen siyan wannan kasaitaccen gida na naira miliyan 540.

KU KARANTA: Badaƙalar satar kuɗi ta yanar gizo: EFCC ta cafke ɗalibai 7

Majiyar NAIJ.com ta bayyana cewar asirin wannan haramtaccen ciniki ya tonu ne a lokacin da sanata Stella Oduah ta shirya bada hayar gidan ne, inda tayi amfani da wani kamfanin dillanci gidaje Daniel Ford & Company Ltd, sa’annan kuma ta amsa mallakar gidan.

Tonon silili: Asirin wata Sanatan Najeriya data sayi gidan naira miliyan 540 a Landan ya tonu

Gidan sanatan

Sai dai majiyar tace dama wanann kamfanin dillancin gidaje wanda dama mallakin wasu yan Najeriya ne mzauna kasar Birtaniya yayi kaurin suna wajen shige ma barayin gwamnatin Najeriya gaba, don ko a binciken tsohuwar ministan man fetur, Allison Maduek da aka yi, sai da aka ambaci sunansa.

Tonon silili: Asirin wata Sanatan Najeriya data sayi gidan naira miliyan 540 a Landan ya tonu

Gidan

Idan za’a iya tunawa ko a zamanin da take minista, an kama Stella Oduah ta laifin satar kudin gwamnati, wanda tayi amfani dasu wajen siyan wasu manyan motocin alfarma kirar BMW a shekarar 2013, wannan ne yayi sanadiyyar da tsohon shuga Jonathan ya sallameta daga gwamnatinsa.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.naij.com

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Hukumar 'yan sanda ta kori wani jami'inta wanda ya harbi direba akan cin hancin naira hamsin

Hukumar 'yan sanda ta kori wani jami'inta wanda ya harbi direba akan cin hancin naira hamsin

Hukumar 'yan sanda ta kori wani jami'inta wanda ya harbi direba akan cin hancin naira hamsin
NAIJ.com
Mailfire view pixel