An sake kwatawa: Ýan bindiga sun bindige wani Ɗansanda a Kaduna

An sake kwatawa: Ýan bindiga sun bindige wani Ɗansanda a Kaduna

- Wani dansandan Najeriya ya gamu da ajalinsa a hannun wasu yan bindiga

- Yanbindigan sun hallaka dansandan a daren Talata a jihar Kaduna

Da safiyar ranar Talata 5 ga watan Satumba ne aka tsinci gawar wani dansanda kwace a unguwar shanu na jihar Kaduna, kusa da kamfanin siyar da motoci na SCOA, inji rahoton Daily Trust.

Majiyar NAIJ.com ta ruwaito an ga alamun harbin bindiga har guda uku a jikinsa, a daidai kirjinsa, cikinsa da kafadarsa, wanda hakan yasa ake ganin ko yaci karo da yan fashi ne a tsakar dare yayin dayake dawowa daga aiki.

KU KARANTA: An nemi Ýansanda 3 an rasa bayan wani harin Ýan-bindiga a jihar Zamfara

Kamar yadda shaidun da suka gawar suka yi bayani, suna ganin a sakamakon kicibus da yayi da yan fashin ne dansandan ya rasa ransa.

Yansanda

Yansanda

Wani shaidan gani da ido ya bayyana cewa “Mun tsinci gawarsa ne a lokacin da muka fito yin sallar Asubahi, nan da nan muka sanar da Yansanda, jama’a na ganin yayi karo da yan fashi ne, inda suka kashe shi suka tafi da bindigarsa.”

Shima Kaakakin yansandan, ASP Mukhtar Aliyu ya tabbatar da faruwar lamarin.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.naij.com

Source: Hausa.naija.ng

Related news
An fara samun sauki a gidajen man fetur da ke birnin tarayya, Abuja

An fara samun sauki a gidajen man fetur da ke birnin tarayya, Abuja

Layin man fetur da ta kuno kai a Abuja ta fara raguwa sosai a halin yanzu
NAIJ.com
Mailfire view pixel