Akeredolu ya sha alwashin kawo karshen zaman banza a jihar Ondo

Akeredolu ya sha alwashin kawo karshen zaman banza a jihar Ondo

Gwamnatin jihar Ondo ta dauki aniyar samar da sababbin masana'antu kuma ta inganta tsofaffin domin kawo karshen zaman kashe wando a tsakankanin matasan jihar.

Kwamishinan kasuwanci da masana'antu na jihar, Otunba Timilehin Adelegbe ne ya bayyana hakan a ranar Talatar da ta gabata yayin ganawa da ma'aikatan sa a babban birni na Akure.

Adelegbe wanda ya karbi aikin na kwamishinan kasuwanci bayan an kaddamar da shi ya ke cewa, ma'aikatar za ta kawo tsare-tsare da zai kawo cigaba ta fuskar samar da aikin yi a fadin jihar.

Akeredolu ya sha alwashin kawo karshen zaman banza a jihar Ondo

Akeredolu ya sha alwashin kawo karshen zaman banza a jihar Ondo

Kwamishinan dai ya yi kira ga ma'aikatan na sa akan jajircewa da kwazo wajen tafiyar da ayyukansu domin sai an tashi tsaye idan ana bukatar tabbatuwar wannan gyara.

KU KARANTA: Akande: Abu ne me wuya samun shugabannin a cikin matasa ma su rikon amana

Ana sa jawabin Dakta Dupe Eshofonie, wanda shine sakatare na din-din-din a ma'aikatar ya bayyana cewa, ma'aikatan ba su da wata matsala kuma yana da kyakkyawar fahimta akan shirinsu na cigaba da aiki nagari da wannan sabon kwashinan.

Domin shawara ko bamu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.naij.com

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://business.facebook.com/pg/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Shin wa ya fi shirga karya, maza ko mata?

Source: Hausa.naija.ng

Related news
An fara samun sauki a gidajen man fetur da ke birnin tarayya, Abuja

An fara samun sauki a gidajen man fetur da ke birnin tarayya, Abuja

Layin man fetur da ta kuno kai a Abuja ta fara raguwa sosai a halin yanzu
NAIJ.com
Mailfire view pixel