Annobar kwalara ta ɓarke a jihar Borno, mutane da dama sun mutu

Annobar kwalara ta ɓarke a jihar Borno, mutane da dama sun mutu

Hukumar kula da cututtuka na Najeriya, NCDC, ta bayyana cewa an samu bullar cutar kwalera a jihar Borno, inda akalla mutane 20 sun mutu, kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.

NCDC ta bayyana cewa annobar ta shafi yankuna shida na jihar, amma tafi tsanani a sansanin yan gudun hijira dake garejin Muna, wanda ke wajen jihar Borno, kamar yadda majiyar NAIJ.com ta ruwaito.

KU KARANTA: An nemi Ýansanda 3 an rasa bayan wani harin Ýan-bindiga a jihar Zamfara

Shugaban NCDC, Chikwe Ihekweazu ya tabbatar da adadin jama’an da suka rasu cikin wata sanarwar daya fitar a ranar 16 ga watan Agusta, inda ya sanar da barkewar cutar a sansanin na yan gudun hijira.

Annobar kwalara ta ɓarke a jihar Borno, mutane da dama sun mutu

Cutar kwalara

Bayan wannan sanarwar ne sai hukumar lafiya ta Duniya tare da wasu hukumomin lafiya suka tabbatar da barkewar cutar.

Ma’aikatar lafiya ta tarayya tare da sauran hukumomin lafiya sun dukufa wajen bada gudunmuwa tare da tallafin don ganin an magance yaduwar cutar. An kafa sansanin magance kwalera a kusa da sansanonin, sa’annan za’a samar da isashshen ruwa a sansanonin” Iniji Ihekweazu

Daga karshe kaakakin yace hukumomin hadin gwiwar zasu yi dukkanin mai yiwuwa wajen yin amfani da duk wasu hanyoyin da suka dace wajen ganin an wayar ma jama’a kai dangane da yaduwar wannan annoba.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.naij.com

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Illar cin hanci: Sojan Najeriya ya bindige wani Mahauci a kan ya hana shi N500 na goro (Hoto)

Illar cin hanci: Sojan Najeriya ya bindige wani Mahauci a kan ya hana shi N500 na goro (Hoto)

Illar cin hanci: Sojan Najeriya ya bindige wani Mahauci a kan ya hana shi N500 na goro (Hoto)
NAIJ.com
Mailfire view pixel