An nemi Ýansanda 3 an rasa bayan wani harin Ýan-bindiga a jihar Zamfara

An nemi Ýansanda 3 an rasa bayan wani harin Ýan-bindiga a jihar Zamfara

Rundunar Yansandan jihar Zamfara ta bayyana cewa sun fara gudanar da neman wasu yansandan su guda 3 da suka bace bayan wani hari da aka kai musu a caji ofis a ranar Litinin 5 ga watan Agusta.

Wannan harin ya faru ne a ranar Litinin a ofishin Yansanda dake kauyen Keta na karamar hukumar Tsafe, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito Kaakakin Yansandan jihar DSP Mohammed Shehu yana fadin.

KU KARANTA: Badaƙalar satar kuɗi ta yanar gizo: EFCC ta cafke ɗalibai 7

Majiyar NAIJ.com ta ruwaito Kaakakin ya musanta sace DPO da Yansanda 3, kamar yadda aka fara yadawa, “Babu wanda aka sace a yayin harin da aka kai mana.” Inji DSP Shehu.

An nemi Ýansanda 3 an rasa bayan wani harin Ýan-bindiga a jihar Zamfara

Yansanda 3

DSP ya cigaba da fadin “ A yanzu haka an aika da jami’an Yansanda na musamman don kurdawa cikin daji da nufin nemo yansanda guda 3 da ba’a gansu ba har yanzu, tare da kamo yan bindigan.”

Majiyar ta kara da cewa yan bindigan sun dira kauyen Keta ne da tsakar ranar Litinin 4 ga watan Satumba dauke da muggan makamai inda suka far ma ofishin Yansandan.

Sai dai daga karshe rundunar Yansandan ta tabbatar da cewa hankali ya kwanta, sa’annan kuma sun tabbatar za’a kamo mutanen da suka kai harin.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.naij.com

An rage matakin shiga jami'a a Najeriya:

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Canji: Hotunan ƙarin sabbin taragon jirgin kasa na Abuja-Kaduna sun iso Najeriya

Canji: Hotunan ƙarin sabbin taragon jirgin kasa na Abuja-Kaduna sun iso Najeriya

Canji: Hotunan ƙarin sabbin taragon jirgin kasa na Abuja-Kaduna sun iso Najeriya
NAIJ.com
Mailfire view pixel