Shugaba Buhari ya taya yan Najeriya murnar fitowa daga matsin tattalin arziki amma yace da sauran aiki

Shugaba Buhari ya taya yan Najeriya murnar fitowa daga matsin tattalin arziki amma yace da sauran aiki

- Shugaba Buhari ya taya 'yan Najeriya farin cikin fitowa daga matsain tattalin arziki

- Shugaban yayi amfani da shafin sa na facebook ne wajen rubuta sakon

- Shugaban yace duk da Najeriya ta fita daga cikin matsin tattalin arzikin, ba zaiyi kasa a gwiwa ba har sai talakwan Najeriya sun ga canjin a gidajensu

Nayi matukar farin ciki da kasar mu Najeriya ta farfado daga matsin tattalin arzikin kuma ina sa ran in ga talakan Najeriya ya samu sauyi.

Amma aikin mu bai kare ba har sai rayuwar dukkan al'umman Najeriya ta inganta.

Ina farin cikin ganin hakar ma ta fara cin ma ruwa amma duk da haka akwai sauran aiki; kuma ba zamu huta ba har sai talakan Najeriya ya shaida cewa an samu canji a kasar.

Shugaba Buhari ya taya yan Najeriya murnar fitowa daga matsin tattalin arziki amma yace da sauran aiki

Shugaba Buhari ya taya yan Najeriya murnar fitowa daga matsin tattalin arziki amma yace da sauran aiki

Babban canjin shine wanda mutane zasu iya gani a kwaryarsu da aljihunnan su ba wai wanda ake fada a fatar baki kawai ba.

DUBA WANNAN: Mahajjata 'yan Najeriya da suka rasu sun kai 14 cikin su harda wani mai'akacin NAHCON

Zamu cigaba da aiki tukuru har sai sun cinma burin mu na inganta rayuwar yan Najeriya.

Ina mika godiya ta gareku domin hakuri da kuma goyon bayan da kuke bamu. Allah ya albarkaci Najeriya da al'ummar ta. Amin.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kana kana da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.naij.com

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Abin da Shugaba Buhari ya fadawa ‘Yan APC na Kasar Inyamurai a Villa

Abin da Shugaba Buhari ya fadawa ‘Yan APC na Kasar Inyamurai a Villa

Abin da Shugaba Buhari ya fadawa ‘Yan APC na Kasar Inyamurai a Villa
NAIJ.com
Mailfire view pixel