Wani uba ya kashe dan sa don ya dage sai ya auri tsohuwa

Wani uba ya kashe dan sa don ya dage sai ya auri tsohuwa

An zargi wani uba a garin Akwa babban birnin jihar Anambra dake a yankin kudu maso gabashin Najeriya da dan sa mai suna Chibuzor saboda ya dage akan lallai shi sai ya auri wata tsohuwa a matsayin mata.

An dai zargi uban da har yanzu mahukunta basu bayyana sunan sa ba da cewa bayan zazzafar muhara tsakanin sa da dan sa kan zancen da ya hau kujerar naki akai sai kuma ya hada baki da wasu sojoji don su zo su bugi dan nasa.

Wani uba ya kashe dan sa don ya dage sai ya auri tsohuwa

Wani uba ya kashe dan sa don ya dage sai ya auri tsohuwa

KU KARANTA: Najeriya ta fita matsin tattalin arziki

NAIJ.com ta samu daga wani da abun ya wakana a gaban sa cewa dan ya suma ne bayan da sojojin da mahaifin ya turo suka gama nada masa dukan tsiya da har ta sa aka garzaya da shi a asibiti.

Tun farko dai majiyar mu ta samu cewa takun saka ya fara shiga tsakanin dan da uban sa ne tun bayan da dan ya kawo wadda yace yana so ya aura a gidan su. Sai dai kuma da ganin matar sai uban ya ca bai yadda ba ya aure ta saboda ta girme masa.

Da aka tambayi jami'an yan sandan jihar sun tabbatar da faruwar lamari.

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Yadda ganawar Shugaba Buhari da Inyamuran APC ta kasance

Yadda ganawar Shugaba Buhari da Inyamuran APC ta kasance

Abin da Shugaba Buhari ya fadawa ‘Yan APC na Kasar Inyamurai a Villa
NAIJ.com
Mailfire view pixel