Za mu maye gurbin likitocin dake yajin aiki da masu yiwa kasa hidima - Ministan Lafiya

Za mu maye gurbin likitocin dake yajin aiki da masu yiwa kasa hidima - Ministan Lafiya

Babban ministan shugaba Buhari na kiwon lafiya, mai suna farfesa Issac Adewale ya bayar da muhimmin umarni ga cibiyoyin lafiya na gwamantin tarayya da ke daukacin fadin kasar nan da su yi amfani da likitoci masu yi wa kasa hidima a halin yanzu da ke cibiyoyin su don cike gurbin likitoci da ke yajin aiki a halin yanzu.

Ministan ya kuma ce daukar wannan matakin ya zama dole ne a gare su domin ganin marasa lafiya da ke cibiyoyin ba su shiga cikin wani yanayin kunci ba kuma ko shakka babu hakan zai bawa gwamnati sukunin yin sulhu da kungiyar Likitocin a kan bukatunsu da suke neman a biya masu.

Za mu maye gurbin likitocin dake yajin aiki da masu yiwa kasa hidima - Ministan Lafiya

Za mu maye gurbin likitocin dake yajin aiki da masu yiwa kasa hidima - Ministan Lafiya

NAIJ.com dai a kwanan baya ta kawo maku labarin cewa kungiyar ta likitoci masu neman kwarewa sun shiga yanjin aikin sai baba ta gani bayan da kwamitin gudanarwar kungiyar suka gama wani taro ba tare da cimma matsaya da gwamnatin tarayya ba.

Haka ma dai a tun watan jiya ma dai kungiyar malaman jami'oin Najeriya ita ma ta kama yajin aiki gadan-gadan.

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Yadda ganawar Shugaba Buhari da Inyamuran APC ta kasance

Yadda ganawar Shugaba Buhari da Inyamuran APC ta kasance

Abin da Shugaba Buhari ya fadawa ‘Yan APC na Kasar Inyamurai a Villa
NAIJ.com
Mailfire view pixel