Tarzoma a tsakanin kungiyoyin dalibai akan yajin aikin ASUU

Tarzoma a tsakanin kungiyoyin dalibai akan yajin aikin ASUU

An yi kacibus tsakanin bangarori biyu na kungiyar daliban Najeriya ( National Association of Nigerian Students, NANS) a babban birni na tarayya.

Dandazon bangare na farko sun taru a wani wurin taro na Unity Fountain dake Abuja, inda suka yi zanga-zanga da nuna rashin goyon bayan su akan wannan yajin aiki na kungiyar ASUU da yake janyowa karatun su zagon kasa da kuma koma baya.

A wani bangaren kuma, wanda Haruna Kadiri ke jagorantar dandazon, sun bayyana goyon bayansu akan wannan yajin aiki akan cewar gwamnatin tarayya ta yi iya ka bakin kokarinta don ganin ta cika sharudda da kungiyar ASUU ta gidanya kafin ta janye yajin aikin.

Tarzoma a tsakanin kungiyoyin dalibai akan yajin aikin ASUU

Tarzoma a tsakanin kungiyoyin dalibai akan yajin aikin ASUU

Shugaban ayarin daliban na farko Ade Abayomi, ya bayyanawa manema labarai na NAIJ.com cewa, su ba tashin hankali ya kawo su ga wannan taro ba sai don kawai su bayyana ra'ayin su.

KU KARANTA: Labarai cikin Hotuna: Aisha Buhari ta bayar da tallafi ga dalibai marayu da marasa karfi a Daura

Kalli bidiyon kicibus din:

Abayomi ya kara da cewa, wannan wurin taro na Unity Fountain dake birnin tarayya shine filin yaki ga duk wani dan Najeriya, domin wuri ne da kowa zai iya bayyana ra'ayin shi, amma sanin kowa ne cewa, Kadiri ba dalibi ba ne da har yake shiga abinda bai shafe shi ba.

Ya ce, "Kadiri ba dalibi bane, in kuma ba haka ba, ya bayyana ma na takardar da take nuna shaidar cewa shi dalibi ne."

Domin shawara ko bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.naij.com

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://business.facebook.com/pg/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Hukumar 'yan sanda ta kori wani jami'inta wanda ya harbi direba akan cin hancin naira hamsin

Hukumar 'yan sanda ta kori wani jami'inta wanda ya harbi direba akan cin hancin naira hamsin

Hukumar 'yan sanda ta kori wani jami'inta wanda ya harbi direba akan cin hancin naira hamsin
NAIJ.com
Mailfire view pixel