Yanzu-Yanzu: Yan bindiga sun farma yan sanda a Bayelsa, sun kashe kuma sun raunata

Yanzu-Yanzu: Yan bindiga sun farma yan sanda a Bayelsa, sun kashe kuma sun raunata

Labaran da ke iso mana yanzu ba da dadewa ba na nuni ne da cewa wasu hatsabiban yan bindiga bata gari sun farwa ofishin yansan yankin Kolo dake a karamar hukumar Ogbia can cikin jihar Bayelsa dake a kudu maso kudancin Najeriya.

Haka ma kuma dai harin na yan bindiga ya haifar da mutuwar wani dan sandan shiyyar guda yayin da kuma da yawa suka jikkata kamar dai yadda muke samun labari.

Yanzu-Yanzu: Yan bindiga sun farma yan sanda a Bayelsa, sun kashe kuma sun raunata

Yanzu-Yanzu: Yan bindiga sun farma yan sanda a Bayelsa, sun kashe kuma sun raunata

KU KARANTA: An rusa tsohon barikin soji a Suleja

NAIJ.com ta kuma samu daga majiyar mu cewa su dai yan bindigar kafin su farma yan sandan sai da suka fara yiwa wani mai kwale-kwale mai a cikin karamar hukumar Ekeremor fashi suka kwace jirgin sa.

Haka kuma dai mahukunta a rundunar yan sandan jihar tace musabbabin kai harin dai shine domin a saci makama kamar dai yadda jami'in hulda da jama'ar rundunar yansandan jihar ya bayyana.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.naij.com Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Canji: Hotunan ƙarin sabbin taragon jirgin kasa na Abuja-Kaduna sun iso Najeriya

Canji: Hotunan ƙarin sabbin taragon jirgin kasa na Abuja-Kaduna sun iso Najeriya

Canji: Hotunan ƙarin sabbin taragon jirgin kasa na Abuja-Kaduna sun iso Najeriya
NAIJ.com
Mailfire view pixel