Manoma na so gwamnatin tarayya ta hana shigo da masara

Manoma na so gwamnatin tarayya ta hana shigo da masara

- Kungiyar manoman Najeriya na so gwamnatin tarayya ta hana shigo da masara cikin kasa

- Kudin masarar da aka shigo da shi Najeriya ya fi na kasashen waje da aka shigo da su tsada

- Gwamnati ya kamata ta samar wa da manoma tallafi a harkar noma

Kungiyar manoman Najeriya sun roka ga gwamnatin tarayya da ta tsayar da shigo da masara cikin kasa.

Mai gudanar da harkokin kungiyar, Mista Redson Tedheke ne ya bayyana hakan a Abuja da nuna cewar yin hakan zai samar wa da manoman karfin gwiwar noma da samun cinikin wanda aka noma a cikin gida.

Shigo da masara kasa ba tare da tantancewa ba yana cikin abin da ke hana samun cinikin na cikin gida da kuma koma baya a canjin da shugaba Buhari yake so a samu a harkar nomar Najeriya.

Manoma na so gwamnatin tarayya ta hana shigo da masara

Manoma na so gwamnatin tarayya ta hana shigo da masara

Dole ne a kare hakkin manoman masara don su cigaba da nomawa don Najeriya ta zama kasa mai zaman kanta a samar da masara ba sai ta shigo da ita daga kasashen waje ba. Kamar yadda gwamnati ta tsayar da shigo da shinkafa haka ya kamata a yi wa masara.

Ba zai yiwu a cewa mutane suje gona ba sannan kuma a cigaba da shigo da kayan gonar daga kasar waje, hakan ba zai samar da riba ba. Idan gwamnati ba tayi saurin daukar mataki ba, zai kashe wa manoman cikin gida kasuwar su da tattalin arzikin kasa.

DUBA WANNAN: 'Yan sanda sun kashe wanda ake zargi da yunkurin kashe wani sanata

Kudin masarar da aka shigo da shi kasa yana yin sauki ne sosai saboda su sauran kasashen gwamnatin su na basu tallafi yadda ya kamata.

Haka gwamnatin Najeriya ya kamata ta yi don tallafawa manoma da samar musu da kayan noma wanda zai sa su sami sauki wajen noma. Hakan zai sa masarar da aka noma cikin gida ta fi wadda aka shigo da ita cikin kasa araha., domin mutanen Najeriya su sayi kayan abinci a sauki.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.naij.com

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Illar cin hanci: Sojan Najeriya ya bindige wani Mahauci a kan ya hana shi N500 na goro (Hoto)

Illar cin hanci: Sojan Najeriya ya bindige wani Mahauci a kan ya hana shi N500 na goro (Hoto)

Illar cin hanci: Sojan Najeriya ya bindige wani Mahauci a kan ya hana shi N500 na goro (Hoto)
NAIJ.com
Mailfire view pixel