Wani saurayi ya gurfana a gaban kuliya bisa laifin lalata da karamar yarinya

Wani saurayi ya gurfana a gaban kuliya bisa laifin lalata da karamar yarinya

A ranar Talatar da ta gabata, wani saurayi Moses Lawal, ya gurfana a gaban wata kotun majistare dake garin Minna babban birnin jihar Neja, bisa laifin aikata lalata da karamar yarinya 'yar shekaru 4 kacal a duniya.

NAIJ.com ta kawo rahoton cewa, lauya daga cibiyar kare hakkin yara Abdullahi Mayaki, shine mai shigar da karar wannan saurayi a gaban kotu, inda ya bayyana cewa, wannan tabokarar ta faru ne a ranar 29 ga watan Agusta a unguwar Soje ta yankin Kpankungu dake karkashin karamar hukumar Chanchaga.

Mayaki ya shaidawa kotu cewa, wannan laifi na saurayi ya saba dokar kasa karkashin sashe na 18, yayin da ita kuma kotu ba ta kama wanda ake tuhuma da aikata wannan laifi ba sabanin kwararan dalilai.

Wani saurayi ya gurfana a gaban kuliya bisa laifin lalata da karamar yarinya

Wani saurayi ya gurfana a gaban kuliya bisa laifin lalata da karamar yarinya

Lauya me shigar da karar wanda ake tuhuma, ya roki kotu akan kar ta bayar da belin wannan saurayi, domin irin laifin da ya aikata ya kai makura na cin zarafi da keta haddi.

KU KARANTA: Wani jami'in dan sanda ya kashe kansa wai don an sauya ma sa wajen aiki zuwa jihar Borno

Shi kuwa alkali mai shari'a Hassan Mohammed, ya daga sauraron karar zuwa ranar 21 ga watan Satumba, kuma ya umarci a cigaba da tsare Moses a gidan kaso.

Domin shawara ko bamu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.naij.com

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://business.facebook.com/pg/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Shin wa ya fi shirga karya, maza ko mata?

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Shugaba Buhari zaije ziyarar aiki kasar Nijar a gobe litinin don bikin cikar kasar shekaru 59

Shugaba Buhari zaije ziyarar aiki kasar Nijar a gobe litinin don bikin cikar kasar shekaru 59

Shugaba Buhari zaije ziyarar aiki kasar Nijar a gobe litinin don bikin cikar kasar shekaru 59
NAIJ.com
Mailfire view pixel