Masu garkuwa da mutane sun sace wani darakta, sun bukaci kudin fansa naira miliyan 40

Masu garkuwa da mutane sun sace wani darakta, sun bukaci kudin fansa naira miliyan 40

- Mau garkuwa da mutane sun sace wani darakta a ma’aikatar ilimi, kimiya da fasaha na jihar Kaduna

- Sun sace shi ne a tsakar daren ranar Lahadi a gidan sa dake Mararaban Rido, Kaduna

- Sun nemi a biya naira miliyan 40 kudin fansa

Wasu masu garkuwa da mutane sun sace wani darakta a ma’aikatar ilimi, kimiya da fasaha na jihar Kaduna, inda suka nemi a basu naira miliyan 40 a matsayin kudin fansa, wani jami’I a ma’aikatar ya bayyana.

An sace daraktan, John Gorah da tsakar daren ranar Lahadi a gidan sa dake Mararaban Rido, Kaduna.

A ranar Talata, 5 ga watan Satumba, mataimakin daraktan, Steven Haruna, ya fada wa kamfanin dillancin labarai na Najeriya (NAN) dake Kaduna cewa masu garkuwan sun kira iyalan mutumin.

Mista Hruna yayi bayanin cewa masu garkuwan sun kai farmaki gidan daraktan, sun yi harbe-harben bindiga a iska domin tsorata mutane sannan suka tsalaka bangon gidan inda suka tafi da Gorah.

KU KARANTA KUMA: Buhari ya samu lafiya, shi zai yi takara a 2019 – APC

Ya kuma bayyana cewa masu garkuwa da mutanen sun sace wata uwa mai shayarwa a makwabta, inda suka bar jaririn da take shayarwa mai makonni uku a duniya.

“Masu garkuwan sun kira iyalan sa inda suka bukaci a basu naira miliyan 40 a matsayi n kudin fansa,” inji shi.

Domin shawara ko bamu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.naij.com Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://business.facebook.com/pg/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gwamnatin Katsina za ta dauka malaman makarantun firamare 5,000

Gwamnatin Katsina za ta dauka malaman makarantun firamare 5,000

Gwamnatin Katsina za ta dauka malaman makarantun firamare 5,000
NAIJ.com
Mailfire view pixel