Duk wani Ibo da ya tsaya takarar shugabancin kasa a 2019 yayi ‘wauta’ – Sanata Utazi

Duk wani Ibo da ya tsaya takarar shugabancin kasa a 2019 yayi ‘wauta’ – Sanata Utazi

- Senata Utazi ya gargadi yan siyaysa Kudu maso gabas akan fitowa takarar shugabankasa a 2019

- Idan Arewa ta kammala lokacin ta Kudu za ta samu damar fitar da shuagabkasa

- Bisa tsarin jam'iyyar PDP a yanzu dan Kudu ba zai iya tsaya takarar shugabankasa a 2019 ba

Sanata mai wakiltan Arewacin Enugu, Chukwuka Utazi, ya gargadi yan siyasa daga Kudu maso gabas akan fitowa takarar shugabancin kasa a zaben 2019.

A lokacin da yake jawabi a Abuja, dan majalisan ya ce ya lura da tsaretsaren jami’iyyar PDP a yanzu, ba za ta ba da goyon bayan fitar da shuagabnakasa daga yanki Kudu maso gabas ba a zaben 2019.

Utazi yace, “Bana sa ran akawai dan kabilan Ibo da zai tsaya takarar shuagabancin kasa a jam’iyyar PDP a 2019.

Duk wani Ibo da ya tsaya takarar shuagabnkasa a 2019 yayi ‘wauta’ – Senata Utazi

Duk wani Ibo da ya tsaya takarar shuagabnkasa a 2019 yayi ‘wauta’ – Senata Utazi

“Maganar gaskiya shine, tsarin jam’iyyar ba zai ba Ibo damar tsayawa takarar shugaban kasa a 2019 ba.

KU KARANTA : Biyafara : Uwazuruike ya bayyana masu daukar nauyin Nnamdi Kanu dan kawo ma neman yanci kabilan Ibo cikas

“Akwai yarjejeniyya a tsakanin Kudu da Arewa. Zai zama wauta idan dan kabilan Ibo ya fito tsayawa takarar shugaban kasa a 2019.

"Nasan Ibo za su samu damar fitar da shugaban kasa idan Arewa ta kammala lokacinta."

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.naij.com

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Shugaba Buhari zaije ziyarar aiki kasar Nijar a gobe litinin don bikin cikar kasar shekaru 59

Shugaba Buhari zaije ziyarar aiki kasar Nijar a gobe litinin don bikin cikar kasar shekaru 59

Shugaba Buhari zaije ziyarar aiki kasar Nijar a gobe litinin don bikin cikar kasar shekaru 59
NAIJ.com
Mailfire view pixel