Akande: Abu ne me wuya samun shugabannin a cikin matasa ma su rikon amana

Akande: Abu ne me wuya samun shugabannin a cikin matasa ma su rikon amana

Tsohon shugaban jam'iyyar APC, Cif Bisi Akande, ya bayyana cewa mawuyacin abu ne, a samu shugabannin kasar nan masu rikon amana daga cikin matasa.

Akande ya bayyana hakan a ranar Litinin din da ta gabata, yayin ganawa da manema labarai a garin Ila Orangun na birnin Osogbo dake jihar Osun, bayan halatar wani majalisi na tattaunawa tare da kungiyar Yarbawa masu kishin kasa.

Jaridar Punch ta ruwaito daga bakin Akande; "akwai cakudanya ta masu munanan dabi'u da kyawawa a cikin matasan mu, sai dai ma su munanan dabi'u sun fi yawa da kuma yin tasiri a cikin al'ummomin mu. Shin ta ya za a samu masu shugabantar kasar nan masu riko da gaskiya a gobe?"

Abu ne me wuya samun shugabannin daga matasa ma su rikon amana

Abu ne me wuya samun shugabannin daga matasa ma su rikon amana

Tsohon shugaban jam'iyyar ya kuma nuna damuwarsa akan yadda ake tafiyar da siyasar kasar nan tamkar mulkin soja.

KU KARANTA: Abin Al'ajabi: Sunan Allah ya bayyana a jikin naman ragon layya

Ya ke cewa, "ana amfani da salo irin na mulkin soja wajen juya akalar jam'iyyu bayan shugabanni sun sauka daga kujerunsu, bayan cewar demukuradiya ake yi a kasar nan."

Ya kuma lura da cewar, mafi yawancin shugabannin jam'iyyu a yanzu sun koyi siyasa ne daga salo irin na lokacin mulkin soja.

Domin shawara ko bamu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.naij.com

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://business.facebook.com/pg/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Shin wa ya fi shirga karya, maza ko mata?

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Yadda ganawar Shugaba Buhari da Inyamuran APC ta kasance

Yadda ganawar Shugaba Buhari da Inyamuran APC ta kasance

Abin da Shugaba Buhari ya fadawa ‘Yan APC na Kasar Inyamurai a Villa
NAIJ.com
Mailfire view pixel