Buhari ya samu lafiya, shi zai yi takara a 2019 – APC

Buhari ya samu lafiya, shi zai yi takara a 2019 – APC

- Magoya bayan jam'iyyar APC sunyi gangami a jihar Ebonyi

- An gudanar da gangamin ne domin nuna goyon baya ga shugaba Muhammadu Buhari a zaben 2019

- Sun kuma ce sun yaba da tsarin mulkin shugaban kasar dari-bisa-dari

A ranar Litinin, 4 ga watan Satumba, jam’iyyar APC sashin jihar Ebonyi tayi gangami a babban birnin jihar, don yakin neman zaen shugaba Buhari a shekarar 2019.

Daga cikin wadanda suka harci gangamin sun hada da ministan kimiya da fasaha, Dr. Ogbonnaya Onu tare da tsohon gwamnan jihar, Cif Martin Elechi.

Shugaban APC na jihar, Eze Nwachukwu ya bayyana cewa sun gudanar da gangamin ne saboda rokon shugaba Buhari kan ya tsaya takarar zabe mai zuwa domin sun yada da tsarin mulkin sa.

Buhari ya samu lafiya, shi zai yi takara a 2019 – APC

Buhari ya samu lafiya, shi zai yi takara a 2019 – APC

A cewarsa babu shakka shugaban kasar ya samu lafiya sannan kuma suna godiya ga Allah bisa wannan ni’ima tasa.

KU KARANTA KUMA: Shugaba Buhari ya yi alkawari ga yan Najeriya

Ya kara da cewa, irin adadin mutanen da suka fito gangamin na nuna cewa jahar Ebonyi mallakar APC ce.

Domin shawara ko bamu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.naij.com

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://business.facebook.com/pg/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Canji: Hotunan ƙarin sabbin taragon jirgin kasa na Abuja-Kaduna sun iso Najeriya

Canji: Hotunan ƙarin sabbin taragon jirgin kasa na Abuja-Kaduna sun iso Najeriya

Canji: Hotunan ƙarin sabbin taragon jirgin kasa na Abuja-Kaduna sun iso Najeriya
NAIJ.com
Mailfire view pixel