Yanzu Yanzu:Najeriya ta fita daga matsin tattalin arziki

Yanzu Yanzu:Najeriya ta fita daga matsin tattalin arziki

- Bayan watanni da dama cikin matsin tattalin arziki, gwamnatin tarayyan Najeriya ta sanar da cewa kasar ta fita daga koma bayan tattalin arziki

- Dr Yemi Kele, shugaban hukumar kididdiga ne ya tabbatar da wannan ci gaban

Hukumar kididdiga ta Najeriya wato National Bureau of Statistics, NBS, ta tabbatar da cewa kasar ta fita daga matsin tattalin arziki.

Dr Yemi Kele, shugaban hukumar kididdiga ne ya tabbatar da wannan ci gaban a safiyar ranar Talata, 5 ga watan Satumba, 2017.

Rahoton ya bayyana cewa tattalin arzikin ya bunkasa da kashi 0.55 cikin 100 a rubu'i na biyu na shekarar 2017 idan aka kwatanta da rubu'i na biyu na shekarar 2016.

Yanzu Yanzu:Najeriya ta fita daga matsin tattalin arziki

Yanzu Yanzu:Najeriya ta fita daga matsin tattalin arziki

Hakan yana nufin cewa girman wannan bunkasa da aka samu ya haura wanda aka samu a rubu'i na biyu na shekarar 2016 da kashi 2.04 cikin 100.

KU KARANTA KUMA: Shugaba Buhari ya yi alkawari ga yan Najeriya

Tattalin arzikin kasar ya samu wannan cigaban ne bayan da ya kwashe rubu'i biyar yana ci gaba da tsukewa.

A lokacin da tattalin arzikin ya bunkasa, ana fitar da gangar danyen mai 1.84m a kowacce rana, inji hukumar.

Ta kara da cewa, baya ga man fetur, harkar noma da inshora da gas da lantarki na cikin abubuwan da suka taimaka wajen bunaksar tattalin arzikin.

Domin shawara ko bamu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.naij.com

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://business.facebook.com/pg/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Shugaba Buhari zaije ziyarar aiki kasar Nijar a gobe litinin don bikin cikar kasar shekaru 59

Shugaba Buhari zaije ziyarar aiki kasar Nijar a gobe litinin don bikin cikar kasar shekaru 59

Shugaba Buhari zaije ziyarar aiki kasar Nijar a gobe litinin don bikin cikar kasar shekaru 59
NAIJ.com
Mailfire view pixel