Shugaba Buhari ya yi alkawari ga yan Najeriya

Shugaba Buhari ya yi alkawari ga yan Najeriya

- Shugaba Buhari yayi alkawarin cigaba da gabatar da

- Ya fadi hakan ne bayan dawowar shi kasar da kyawawan tsammani

- Yayi alkawarin cigaba da ayyuka da zasu amfani yan Najeriya

Shugaba Muhammadu Buhari ya tabbatar wa yan Najeriya da alkwarin cigaba da yi wa kasar bauta. Ya kuma yi nuni cewa rashin lafiyarshi daga Allah ne.

Garba Shehu ne ya fadi hakan a wani jawabi da ya gabatar a ranar Litinin, 4 ga watan satumba.

A yayinda shugaba Muhammadu Buhari ya tarbi kungiyoyin manoma, yan kasuwa, matasa da dattawan siyasa a gidansa dake Katsina, yace ya dawo kasar cikin tsammani da karfin cigaba da gudanar da ayyuka domin inganta rayukan mutane da gyara kasar Najeriya don cigaban kasar.

Shugaba Buhari ya yi alkawari ga yan Najeriya

Shugaba Buhari ya yi alkawari ga yan Najeriya

“Game da wassu kalubale da kasar ke fuskanta, muna iyakacin kokarinmu domin tabbatar da matakai da zasu maganta matsaloli, kuma zamu cigaba da iyakacin kokarinmu.

KU KARANTA KUMA: Shugaba Buhari na kallon wasan Najeriya da Kamaru (hotuna)

“Nayi murna da zuwanku yau, kuma ina muku godiya kan addu’a da kuka yi mun. Ku shuwagabannin kungiyoyi ne a matakai daban daban, kun fi kusa da mutane shi yasa zaku fahimci wadannan matsalolin. Muna bukatan goyon bayanku’’. Inji shi

A jawabinsa, shugaban kungiyoyin, Zannan-Daura, Alhaji Sani Ahmed Daura, yace dawowan shugaban ya kasance ikon Allah da kuma juyi ga albarkatun kasan.

“A madadin dattawan wannan taron, muna mika wa Allah godiya da dawowanka a raye, da koshin lafiya’’.

Daura, tsohon mataimakin shugaban yan sanda, yace shugaban kasan ya kasance mai hakuri da juriya, ya kara da addu’a cewa Allah kara mishi karfi da hikiman shugabantan wannan kasan

Domin shawara ko bamu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.naij.com

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://business.facebook.com/pg/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
An fara samun sauki a gidajen man fetur da ke birnin tarayya, Abuja

An fara samun sauki a gidajen man fetur da ke birnin tarayya, Abuja

Layin man fetur da ta kuno kai a Abuja ta fara raguwa sosai a halin yanzu
NAIJ.com
Mailfire view pixel