Buhari ya mika ta'aziyyar sa ga Kasimu Yero da Luther Cishak

Buhari ya mika ta'aziyyar sa ga Kasimu Yero da Luther Cishak

- Shugaba Muhammadu Buahari ya mika ta'aziyyar sa ga iyalin Kasimu Yero

- Shugaban ya sake mika ta'aziyyar sa a rashin babban ShugabaLuther Cishak

-Shugaba Luther Cishak shugaba ne mai son zaman lafiya tsakanuin al'umma

- Shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya mika ta’aziyyar sa ga shahararren dan wasan kwaikwayo Kasimu Yero, wanda ya rasu bayan jinyar rashn lafiya da ya yi.

Buhari ya shaida cewa lallai dandalin Kannywood zasu yi babban rashin dan wasa. Ya musalta Kasimu Yero a matsayin wani babban dan wasa mai fasaha a zamanin sa.

Shugaban ya mika ta’aziyyar sa ga iyalin marigayin tare da addu’ar Ubangiji ya gafarta masa. Kasimu yero ya rasu a Kaduna ranar lahadi, ya rasu yana da shekara 70 ya bar ‘ya’ya takwas a duniya.

Buhari ya mika ta'aziyyar sa ga Kasimu Yero da Luther Chisak

Buhari ya mika ta'aziyyar sa ga Kasimu Yero

Shugaban ya sake mika ta’aziyyar sa ga Shugaban kungiyar addinin kirista na Najeriya, Reverend Luther Dabirong Cishak.

Mai magana da yawun shugaban kasa, Malam Garba Shehu ya musalta marigayin a matsayin wani babban shugaban addini a Najeriya.

DUBA WANNAN: Hare-haren Boko Haram na cigaba a watannin da suka gabata

Marigayin ya rasu yana da shekara 88 wanda lokacin rayuwarsa mutum ne mai saon zaman lafiya tsakanin musulmai da kafairai a Plateau da kasa baki daya.

Shugaban ya shaida taimakon da Cishak yayi a shekarar 2003 da rikici ya barke tsakanin musulmai da kafirai a jihar Plateau. Buhari ya mika ta’aziyyar sa ga iyalin Cishak don babban rashin da suka yi.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.naij.com

Source: Hausa.naija.ng

Related news
An fara samun sauki a gidajen man fetur da ke birnin tarayya, Abuja

An fara samun sauki a gidajen man fetur da ke birnin tarayya, Abuja

Layin man fetur da ta kuno kai a Abuja ta fara raguwa sosai a halin yanzu
NAIJ.com
Mailfire view pixel