Buhari ya bada umurnin hada layin dogo na jirgin kasa zuwa jihohi 36, da Abuja

Buhari ya bada umurnin hada layin dogo na jirgin kasa zuwa jihohi 36, da Abuja

- Shugaba Muhammadu Buhari ya ba da umurnin hada jihohi 36 da Abuja ta hanyar jirgin kasa

- Ministan sufuri, Rotimi Ameachi ne ya bayyana hakan a taron kungiyar sufuri ta kasa karo na 15 a Sokoto

- Ya bayyana cewa wannan ayyuka na jirgin kasa a kasar zai samar da ayyukan yi ga matasa

Ministan sufuri, Rotimi Ameachi, ya bayyana cewa shugaba Muhammadu Buhari ya umurce shi da ministan wutar lantarki, ayyuka da gidaje, Babatunde Fashola da su hada jihohin tarayya 36 da babban birnin tarayya ta hanyar jirgin kasa.

Ameachi ya bayyana hakan ne a lokacin taron kungiyar sufuri ta kasa karo na 15, a jihar Sokoto.

Ya ce, “Shugaban kasar ya kiramu mu biyu, ni da abokin aikina dake ma’aikatar wutar lantarki, ayyuka da gidaje, Babatunde Fashola, sannan ya sanar dani cewa na tabbatar da cewa an hada jihohin kasar 36 harda Abuja ta hanyar jirgin kasa”.

Ya kara da cewa ayyukan jirgin kasa dake gudana a kasar yanzu zai samar da ayyukan yi ga matasa.

Buhari ya bada umurnin hada layin dogo na jirgin kasa zuwa jihohi 36, da Abuja

Buhari ya bada umurnin hada layin dogo na jirgin kasa zuwa jihohi 36, da Abuja

Ya bayyana cewa don habbaka tattalin arziki sosai, ya zama dole a inganta tashar jirgin kasa.

KU KARANTA KUMA: Tsoro a Abia yayinda yan kungiyar IPOB suka kara da sojoji

Ameachi yace gwamnatin tarayya na gab da shiga yarjejeniya da tashoshin jiragen kasa a fadin kasar don tabbatar da cewa an fara amfani dasu nan dad an wani lokaci kadan.

Ameachi ya kuma bayyana cewa shugaban kasar ya amince da gina tashar jirgi na Abuja-Itakpe, yayinda ake shirye-shirye don fara aiki a tashar Ajaokuta-Warri wanda za’a kammala a watan Yunin 2018.

Domin shawara ko bam u labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.naij.com

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://business.facebook.com/pg/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Layin man fetur da ta kuno kai a Abuja ta fara raguwa sosai a halin yanzu

Layin man fetur da ta kuno kai a Abuja ta fara raguwa sosai a halin yanzu

Layin man fetur da ta kuno kai a Abuja ta fara raguwa sosai a halin yanzu
NAIJ.com
Mailfire view pixel