Kallon kwallon Shugaba Buhari ta jawo ka-ce-na-ce

Kallon kwallon Shugaba Buhari ta jawo ka-ce-na-ce

- A jiya ne Kasar Najeriya ta buga wasa da Kasar Kamaru a Yaounde

- Shugaban kasa Buhari yana cikin wanda su ka kalli wasan cikin dare

- Jama'a sun yi mamakin ganin Shugaban kasar da karamin talabiji

Jama'a na ta ce-ce-ku-ce bayan an ga hotunan Buhari yana kwallon wasan Najeriya jiya a gidan sa a Daura.

Kallon kwallon Shugaba Buhari ta jawo ka-ce-na-ce

Shugaba Buhari yana kwallon Super Eagles

Mai magana da bakin Shugaban kasar Femi Adesina ne dai ya dauki hotunan a inda Najeriya ta buga kunnen doki da makwabta Kamaru. Wasu dai sun ce ya kamata ace akwatin talabijin Shugaban kasar ya fi haka girma kuma a samu dan zamani.

KU KARANTA: Buhari ya gana da MC Tagwaye a Daura

Akwai wanda ya maida martani yana cewa ya kamata ace Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya samu 'yar karamar riga ya rika sanyawa domin ya rika shan iska a cikin gida. Shugaban kasar dai ya zuba wata doguwar farar riga ne a a yayin da yake shakatawar.

A jiyan Shugaban kasa Muhammadu Buhari yayi alkawarin ganin 'Yan Najeriya sun ji dadi a mulkin sa yace zai cigaba da yin bakin kokarin sadon kuwa ya dawo da himma.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.naij.com

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Bidiyo game da karon Najeriya da Kamaru

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Shugaba Buhari zaije ziyarar aiki kasar Nijar a gobe litinin don bikin cikar kasar shekaru 59

Shugaba Buhari zaije ziyarar aiki kasar Nijar a gobe litinin don bikin cikar kasar shekaru 59

Shugaba Buhari zaije ziyarar aiki kasar Nijar a gobe litinin don bikin cikar kasar shekaru 59
NAIJ.com
Mailfire view pixel