An shiga rudani saboda rusa bariki a Suleja

An shiga rudani saboda rusa bariki a Suleja

- Gwamnanti ta ba da sanarwar watanni uku kafin aka rusa barikin

- Tsofaffin Sojojin da suka yi ritaya da ma'aikatan farar hula ke zama a barikin

- Maikatan jam'ian tsaro daban-daban suka samar da tsaro lokacin rusa barkin

A jiya litinin 5 ga watan Satumba 2017, aka rusa tsohon barikin sojoji dake Suleja jihar Neja.

An kawo buldoza, tare da ma’aikatan jam’ian tsaro daban-daban dan samar da tsaro a lokacin da ake rushe rushen.

Jamian tsaro sun isa wajen ne da misalin karfe 7 na safiya, suka umarci mazauna barikin da su fita daga gidajen su, ba tare da ba su lokacin fitar da kayan su ba, inji wani mazaunin wurin.

Mazaunan gurin, wanda kunshi tsofaffin sojojin da suka yi ritaya, da kuma ma'aikatan farar hula da suka sun koka da cewa duk abubuwan da suka mallak an birne su a cikin gidajen su da aka rusa.

An shiga rudani saboda rusa bariki a Suleja

An shiga rudani saboda rusa bariki a Suleja

Yawancin mutanen da ke zama a barikin sunce sun dade suna zaune a wurin, sunyi korafin cewa ba su san inda za su koma ba, basu san ta yadda za su fara sabuwar rayuwa ba saboda rashin kudi.

KU KARANTA : Biyafara : Uwazuruike ya bayyana masu daukar nauyin Nnamdi Kanu dan kawo ma neman yanci kabilan Ibo cikas

Mai magana da yawun jami'in watsa labarai na Suleja, Malam Jibrin Bisallah, ya ce an gina barikin ne a shekarar 1970 domin wasu sojoji bayan yakin basasa don amfani da shi wajen wucin gadi, kafin a kammala aikin barikin soja na Kontagora, shima a Jihar Neja .

Ya ce gwamnatin da ta gabata ta biya sojoji nda suka yi gini a filin barikin diyyar naira miliyan N50, kuma amba ma mazaunan wajen wa’adin watanni uku su tashi kafin a rusa barkin, amma an kasa rusawa sai sai yanzu saboda rikicin da mutanen ke yi duk lokacin da aka je rusawa.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.naij.com

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Shekau ya fito da sabuwar bidiyo

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Hotuna: Shugaba Buhari ya dawo daga kasar Faransa inda ya halarci taro a kan dumaman yanayi

Hotuna: Shugaba Buhari ya dawo daga kasar Faransa inda ya halarci taro a kan dumaman yanayi

Hotuna: Shugaba Buhari ya dawo daga kasar Faransa inda ya halarci taro a kan dumaman yanayi
NAIJ.com
Mailfire view pixel