Wani jami'in dan sanda ya kashe kansa wai don an sauya ma sa wajen aiki zuwa jihar Borno

Wani jami'in dan sanda ya kashe kansa wai don an sauya ma sa wajen aiki zuwa jihar Borno

A can birnin Abakaliki dake jihar Ebonyi, wani jami'i na 'yan sanda , Donatus Oyibe, ya yi sanadiyar kashe kansa wai don a canja ma sa wajen aiki zuwa jihar Borno

NAIJ.com ta samu rahotonnin cewa, Mista Oyibe wanda mazauni kuma dan asalin karamar hukumar Ndegu Ishieke ta jihar Ebonyi, ya tsunduma kansa cikin wata rijiya a daren ranar Lahadin da ta gabata, yayin da ya fita debo ruwa.

Mazauna wannan yanki sun ruwaito cewa, tun lokacin da Oyibe ya karbi takardar sauyin wajen aiki zuwa jihar Borno a ranar 28 ga watan Agusta, ya shiga wani hali na damuwa da kuma kunci.

Daga wata majiya ta 'yan sandan, Obiye yana daya daga cikin jami'ai na kwana-kwanan nan da ka maido su zuwa garin Abakaliki bayan sun kammala wani aikin zagaye, majiyar kuma ta ce, Obiye mutum ne mai kwazon aiki domin har ya fara aikinsa cikin gaggawa a ma'aikatarsu dake birnin na Abakaliki.

Wani jami'in dan sanda ya kashe kansa wai don an canja ma sa wajen aiki zuwa jihar Borno

Wani jami'in dan sanda ya kashe kansa wai don an canja ma sa wajen aiki zuwa jihar Borno

Ita kuwa 'ya ga marigayin, Ukamaka, ta bayyana cewa, mahaifin na ta ya dauki bokiti domin debo ruwa a rijiya, inda bayan wani lokaci mai tsawo aka bi sawaunsa ganin cewa bai dawo ba.

KU KARANTA: Zaben 2019: Obasanjo na shirin tsayar da El-rufa'i shugaban kasa

Ta ce, isar su bakin wannan rijiya suka riski botikin amma ba bu ko alamar mahaifin ta, nan fa aka bazama cikin bincike har aka gano gawar sa a cikin wannan rijiya..

A yayin da aka tuntubi kakakin 'yan sandan jihar, Loveth Ogah, ya bayyana cewa har yanzu ba ta samu rahoton faruwar wannan abu ba, amma ta yi alkawari zayyanawa manema labarai da zarar sun gudanar da bincike akan wannan lamari.

Domin shawara ko bamu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.naij.com

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://business.facebook.com/pg/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Shin wa ya fi shirga karya, maza ko mata?

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Ashe Iran ke baiwa 'yan tawayen Yemen makaman yaki

Ashe Iran ke baiwa 'yan tawayen Yemen makaman yaki

Ta tabbata' Kasar Iran ke taimakawa 'yan tawayen Kasar Yemen
NAIJ.com
Mailfire view pixel