Fayose ya kori babban hadiminsa kan Sallar idi

Fayose ya kori babban hadiminsa kan Sallar idi

- Gwamna Fayose ya tsige sakateren yada labaran sa, Idowo Adelusi

- Ya tsige Adelusi ne bisa dalilin rashin gabatar da manema labarai da zasu kasance cikin tawagar gwamnan zuwa masallacin idi a ranar Sallah

Gwamna Ayodele Fayose na jihar Ekiti ya tsige babban sakateren labaran sa, Idowu Adelusi, a dogon hutun bikin sallah.

Ko da yake, jawabi bai bayyana dalilin ba da yasa aka tsige shi, amman majiyan gwamnan sunyi ikirarin cewa sauke shi daga mukaminsa baya rasa nasaba da al’amarin da ya auku a ranar sallah.

Jaridar Punch ta rahoto cewa majiyan gwamnan sunyi ikirarin cewa an sauke Adelusi ne saboda rashin gabatar da isasshen manema labarai ga tawagar gwamna a masallacin idi, a ranar Juma’a.

Fayose ya kori babban hadiminsa kan Sallar idi

Fayose ya kori babban hadiminsa kan Sallar idi

Mataimakin gwamnan a kafofin yada Labarai, Lere Olayinka bai dai bayyana dalilin dake tattare da tsige Alusi da aka yi ba.

KU KARANTA KUMA: Tsoro a Abia yayinda yan kungiyar IPOB suka kara da sojoji

Haka Zalika, NAIJ.com ta rahoto a baya cewa an dakatar da dan majalisa mai wakiltan mazabar Ekity-East a majalisan dokokin jihar Ekiti Hon. Fajana Ojo-Ade, har na tsawon kwana 101 ba tare da biya ba.

A lokacin dakatarwa an hana dan majalisan zuwa harabar majalisan sai ya nuna sa hannu da ya bashi damar yin haka.

Domin shawara ko bamu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.naij.com

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://business.facebook.com/pg/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Shugaba Buhari zaije ziyarar aiki kasar Nijar a gobe litinin don bikin cikar kasar shekaru 59

Shugaba Buhari zaije ziyarar aiki kasar Nijar a gobe litinin don bikin cikar kasar shekaru 59

Shugaba Buhari zaije ziyarar aiki kasar Nijar a gobe litinin don bikin cikar kasar shekaru 59
NAIJ.com
Mailfire view pixel