Mafi yawan manoma sun yi gaba da bashin CBN na noman shinkafa

Mafi yawan manoma sun yi gaba da bashin CBN na noman shinkafa

- Manoma da sama sun ci bashin Gwamnati sun yi kafa

- Kadan daga cikin manoma kasar su ka biya bashin CBN

- Kungiyar manoma na kasar ta bayyana wannan kwanan nan

Jaridar Premium Times tace mafi yawan manoma sun tsere da kudin Gwamnati a Najeriya bayan sun karbi bashi.

Mafi yawan manoma sun yi gaba da bashin CBN na noman shinkafa
Manoman shinkafa sun yi gaba da kudin Gwamnati
Asali: UGC

Bai fi dai kashi 1% ne na cikin 100 su ka maidawa Gwamnati bashin da su ka karba na noma ba a shekarar bara kamar yadda Kungiyar manoman kasar watau AFAN ta fada ta bakin Shugaban ta na Jihar Kano Faruk Rabiu.

KU KARANTA: Ana zargin 'Yan Sanda da cin hanci

Mafi yawan manoma sun yi gaba da bashin CBN na noman shinkafa
Shugaba Buhari wajen noman shinkafa

Alhaji Rabiu yace cikin mutane sama da 5, 540 da su ka karbi bashin babban bankin kasar na CBN domin noman shinkafa bai fi manoma 50 ne rak su ka biya bashin da su ka ci ba inda sauran su kayi gum.

Shugaban manoman na Jihar Kano yace idan aka cigaba da tafiya a haka Gwamnati ba za ta kara ba manoma bashi ba.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Auren Sarkin Ile Ife ya mutu

Asali: Legit.ng

Online view pixel