Abin da ya sa mutane suke watsa labaran karya akan Buhari - Adesina

Abin da ya sa mutane suke watsa labaran karya akan Buhari - Adesina

- Femi Adesina yayi fashin baki akan dalilan da yasa wasu mutane ke yiwa shugaba Buhari kage

- A cikin bayanan nasa ya lisafa kiyaya, hassada da kokarin tada zaune tsaye a cikin dalilan

- Ministan al'adu Lai Mohammed yayi tir da labarin kagen da ke yawo a kafofin yadda labarai na cewa Buhari zai tafi Amurka

Mai ba Shugaban kasa shawara ta musamman akan kafofin sadarwa da watsa labarai, Femi Adesina, ya ce duk wanda ya watsa labaran kage akan shugaban kasa yayi hakan ne da nufin muzanta shugaban da janyo kiyayya akan shugaban sa.

Dalilan da yasa wasu mutane ke yada jita-jita akan Buhari - Adesina

Dalilan da yasa wasu mutane ke yada jita-jita akan Buhari - Adesina

A cewar sa akwai dalilai da dama na watsa labaran kage amma wannan tsabar mugunta ne kawai. Ya fadi haka me a daran litini a gidan talabijin na channels Television a cikin shirin 'siyasar mu a yau' wanda Seun Okinbaloye ya gabatar

DUBA WANNAN: El-Rufai bashi da ladabi, bai san girman manya ba - Edwin Clark

Yayi wannan jawabi ne bisa ga yadda gwamnati ta nuna damuwarta kan yadda ake watsa labaran kage da maganganun kiyayya a kafofin yada labarai wanda hakan yana wasa da kasancewar mu al'umma daya

A ranar lahadi ne ministan yada labarai da kuma Al'adu, Lai Muhammad ya yi tir da labarin kagen da ya shahara a kafofin watsa labarai cikin lokaci kankani cewa shugaban kasa zai tafi kasar Amurka. Adesina a game da wannan labari cewa yayi an kagi wannan labari ne don a jawo karan tsana akan shugaban kasa.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kana kana da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.naij.com

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Ashe Iran ke baiwa 'yan tawayen Yemen makaman yaki

Ashe Iran ke baiwa 'yan tawayen Yemen makaman yaki

Ta tabbata' Kasar Iran ke taimakawa 'yan tawayen Kasar Yemen
NAIJ.com
Mailfire view pixel