'Yan sanda sun kashe wanda ake zargi da yunkurin kashe wani sanata

'Yan sanda sun kashe wanda ake zargi da yunkurin kashe wani sanata

- 'Yan sanda sun kashe wani mutum da ake zargi da yunkurin kashe wani sanata

- Wasu 'yan fashi sun addabawa mutan garin Ihima

- 'Yan sanda sun kama wasu mutane da suke aikata laifi da Kwamandan

‘Yan sandan jihar Kogi sun kashe wani mutum da suke hari tun-tuni, mutumin dan fashi ne kuma yana garkuwa da mutane.

Kwamishinan ‘yan sanda, Wilson Inalegwu ya ce ‘yan Special Anti-Robbery Squad (SARS) ne suka kama mutumin mai suna Lukman a Obeiba, nan suka harbe shi ya fadi matacce.'

'Yan sanda sun kashe wanda ake zargi da yunkurin kashe wani sanata

'Yan sanda Najeriya a bakin aiki

Kwamishinan ya ce 'Lukman da mukarrabansa da suka hango ‘yan sandan sai suka bude musu wuta, hakan ya sa ‘yan sandan suka mayar musu da harbi.'

‘Yan sandan sun cafke wasu mutum shida da suke zargi da aikata laifin tare da Lukman wanda suke wa lakani da Kwamanda.

Lukman yana cikin mutanen da suka yi yunkurin kashe Sanata Dino Melaye a gidan shi da ke Ayetoro Gbede a watan Afrilu. Nan ne ‘yan sanda suka bazama neman sa don yana da tarihin fashi da garkuwa da mutane.

Wasu daga cikin abokan huldar lukman din sun tsallake rijiya da baya, sun kwace daga hannun ‘yan sanda sun hadu su kai wa mutanen unguwa hari sun ruguzawa ‘yan sandan motar su da ofishin su.

DUBA WANNAN: Jihohin da suka fi sauran jihohi ma'aikata gwamnati

‘Yan sandan sun cigaba da zama bakin aikin su don samar da tsaro a unguwar da kuma kokarin kamo mutanen da suka kai harin.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.naij.com

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Layin man fetur da ta kuno kai a Abuja ta fara raguwa sosai a halin yanzu

Layin man fetur da ta kuno kai a Abuja ta fara raguwa sosai a halin yanzu

Layin man fetur da ta kuno kai a Abuja ta fara raguwa sosai a halin yanzu
NAIJ.com
Mailfire view pixel