Boko Haram ta kashe mutane sama da 200 tun daga watan Afrilu

Boko Haram ta kashe mutane sama da 200 tun daga watan Afrilu

- Amnesty International ta fitar da kiyasin mutanen da maharan Boko Haram suka kashe tun daga watan Afrilu

- Kokarin kawar da Boko Haram bai hana su cigaba da kai hare-hare ba

- Boko Haram tana anfani da mata wajen kai harin kunar bakin wake

Kungiyar Amnesty International tana dauke da dokar rashin muzgunawa mutane da ake da cin zarafi da tare hakkin dan Adam. Musamman daga hare-haren da mayakan Boko Haram suke kai wa tun 2010.

Daga kungiyar Amnesty sun ce mutuwar mutane ta karu ne daga watan Afrilu in aka kwatanta da shekarar 2016 a arewa maso gabashin Najeriya da Kamaru musamman daga ‘yan kunar bakin wake.

Boko Haram ta kashe mutane sama da 200 tun daga watan Afrilu

Boko Haram ta kashe mutane sama da 200 tun daga watan Afrilu

Kungiyar ta hada ta fitar da rahoton cewa hare-haren da maharan ke kai wa ya cigaba ne in aka kwatanta da lokutan da suke kai hari a 2016. Yawancin hare-haren ta kunar bakin wake ne da suke sa ‘yan kananan yara suke aikatawa.

Duk da kokarin da sojin Najeiya da kasashen kewaye suke yi na ganin an kawar da Boko Haram bai hana maharan cigaba da kashe mutane ba.

A kalla Boko Haram sun kashe mutane sama da 100,000 tun daga shekarar 2009 daga kididdigar da Amnesty International ta yi.

DUBA WANNAN: Dubi kasashe 25 da suka fi kowa karfinn soji

Harin da yafi muni shine harin da suka kai wa mahakan mai a Magumeri a jihar Borno wanda suka kashe mutane 40 suka sace wasu mutum 3.

Boko Haram ta kai hare-hare a kalla sau 10 a kauyen Diffa da ke Niger a tun daga farkon shekarar 2017.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.naij.com

Source: Hausa.naija.ng

Related news
An fara samun sauki a gidajen man fetur da ke birnin tarayya, Abuja

An fara samun sauki a gidajen man fetur da ke birnin tarayya, Abuja

Layin man fetur da ta kuno kai a Abuja ta fara raguwa sosai a halin yanzu
NAIJ.com
Mailfire view pixel