Assha! Karanta yadda albasa tayi sanadiyyar mutuwar mutane 7 a jihar Zamfara

Assha! Karanta yadda albasa tayi sanadiyyar mutuwar mutane 7 a jihar Zamfara

Mutanen cikin garin karamar hukumar Shinkafi dake a jihar Zamfara sun tashi da wani mummunan labari bayan da suka wayi gari da rashin wasu mutane 6 ringis yan gida guda bayan kammala cin wani abincin gargajiya mai suna 'fate-fate'.

Labaran farko farkon da kuma aka samu daga mahukunta dai yanzu shine abincin nasu an yi shi ne da wata albasa ne da ake kyatata zaton tana dauke da guba a cikin ta wanda jim kadan bayan cin abincin ne suka fara rashin lafiyar da har tayi ajalin su.

Assha! Karanta yadda albasa tayi sanadiyyar mutuwar mutane 7 a jihar Zamfara

Assha! Karanta yadda albasa tayi sanadiyyar mutuwar mutane 7 a jihar Zamfara

KU KARANTA: Sanata Shehu Sani ya shawarci shugaba Buhari

NAIJ.com ta samu dai cewa a cikin wadanda suka gamu da ajalin nasu hadda wata diyar makwaftan su da Allah yasa tayi rashin sa'ar cin abincin a gidan.

Sai dai kuma mun samu labarin cewa kishiyar matar gidan da ba girkin ta bane a ranar ita bata ci abin cin ba kuma Allah ya taimake ta ta tsallake rijiya da baya amma sai dai duka yayan ta sun rasu.

Da majiyar mu ta tuntubi jami'in hulda da jama'a na yan sandan jihar DSP Muhammad Shehu ya tabbatar da aukuwar lamarin inda kuma yace yanzu haka suna kan bincike ne.

Source: Hausa.naija.ng

Related news
An zargi Abba Kyari a kan ajiyar biliyan 50 na NNPC a bankuna wanda ta sabawa tsarin asusun TSA

An zargi Abba Kyari a kan ajiyar biliyan 50 na NNPC a bankuna wanda ta sabawa tsarin asusun TSA

An zargi Abba Kyari a kan ajiyar biliyan 50 na NNPC a bankuna wanda ta sabawa tsarin asusun TSA
NAIJ.com
Mailfire view pixel