Tsoro a Abia yayinda yan kungiyar IPOB suka kara da sojoji

Tsoro a Abia yayinda yan kungiyar IPOB suka kara da sojoji

- Mazauna garin Umuahia na cikin tashin hankali sakamakon karo tsakanin yan kungiyar IPOB da sojoji

- Al'amarin ya afku ne a daren ranar Alhamis

- Tuni yan kasuwa sun kulle shagunansu don gudun karda al'amarin ya cika da su

Al’umman garin Umuahia, babban birnin jihar Abia sun shiga tashin hankali a daren ranar Litinin, bayan mambobin kungiyar masu fafutukar neman yankin Biyafara sun yi mummunan karo da sojoji.

Al’amarin wanda aka ce ya afku a Isi Gate ya yadu zuwa sauran yankunan jihar, inda ya sanya tsoro a zukatan mazauna jihar da kuma baki.

Majiyoyi a Umuahia, sun bayyana cewa al’amarin ya tursasa yan kasuwa da sauran masu sana’oí a birnin rufe shagunansu domin tsoron karda a hada dasu wajen yin kame.

Yayinda ake kokarin hada bayanai akan rahoton, wani rahoto ya nuna cewa wasu sojoji dake Isi Gate ne ke karban kudi daga masu adaidaita sahu sai daya daga cikin masu adaidaitan yaki basu kudi, shine daya daga cikin sojojin ya kwashe shi da mari.

Tsoro a Abia yayinda yan kungiyar IPOB suka kara da sojoji

Tsoro a Abia yayinda yan kungiyar IPOB suka kara da sojoji

Al’amarin ya zamo rikici lokacin da mambobin kungiyar suka far ma sojojin.

KU KARANTA KUMA: Zaben 2019: Obasanjo na shirin tsayar da El-rufa'i shugaban kasa

Wani rahoton kuma ya yi ikirarin cewa sojojin dake tashar su dake kusa da Isi Gate sun tsayar dad an adaidaitan sannan kuma bukaci dreban ya basu tutar Biyafara da IPOB dake cikin adaidaitan sa, amma sai dreban ya ki.

Wannan ne ya kawo musayar yawu a tsakaninsu harma ya janyo hankali dandazon jama’a, ganin cewa mutane sun taru, sai sojojin sukayi harbi a iska domin su tsorata mutane, amma sai mutanen suka far masu harma suka ji ma wasun daga cikinsu rauni.

A lokacin wannan rahoton, an tattaro cewa hukumomin tsaro sun cike birnin jihar domin hana karya doka a birnin.

Shugaban kungiyar IPOB na jihar, Mista Ikechukwu Ugwuoha ya bayyana cewa ba’a koro mai bayani akan al’amarin ba tukuna.

Amma wani dan kungiyar da ya nemi a sakaya sunan sa ya fada wa manema labarai cewa sojoji ne suka yi harbio sannan suka ji ma wasu mutane rauni, alhalin mutanen basu neme su da fada ba kawai suna koron su ne das u saki mutumin tunda basu same shi da wani aibu ba.

Jami’in hulda da jama’a na birgediya 14, Manjo Oyegoke Gbadamosi ya bayyana cewa anji ma wasu sojoji rauni sannan kuma suna wani asibiti da ba’a bayyana ba inda suke samun kulawar likita.

Domin shawara ko bamu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.naij.com

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://business.facebook.com/pg/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Ashe Iran ke baiwa 'yan tawayen Yemen makaman yaki

Ashe Iran ke baiwa 'yan tawayen Yemen makaman yaki

Ta tabbata' Kasar Iran ke taimakawa 'yan tawayen Kasar Yemen
NAIJ.com
Mailfire view pixel