Wani saurayi ya gamu da ajalin sa bayan yasha duka a gasar sharo

Wani saurayi ya gamu da ajalin sa bayan yasha duka a gasar sharo

Wani saurayin bafullatani mai suna Yari Inusa ya gamu da ajalinsa bayan da ya sha duka a yayin gasar wasan gargajiyar nan na sharo da aka saba gudanar wa a duk shekara tsakanin yan kabiran fulani.

Kamar dai yadda labarin ya same mu, lamarin ya faru ne a wani kauye da ake cewa Durmin Biri a cikin karamar hukumar Kafur ta jihar Katsina.

Wani saurayi ya gamu da ajalin sa bayan yasha duka a gasar sharo

Wani saurayi ya gamu da ajalin sa bayan yasha duka a gasar sharo

KU KARANTA: Babangida ya yaba da salon mulkin Buhari

NAIJ.com ta samu dai cewa kamar yadda aka saba mazaje samari biyu da ke neman auren budurwa ne kan hunce a buge su a lokacin gasar da nufin gano wanda zai lashe daga karshe kuma ya auri yarinyar.

To sai dai a wannan karon lamarin ya zo a ba zata ne yayin da abokin sharon na Yari Inusa mai suna Ahmad Sa'idu ya maka masa bulala a kan sa maimakon a jikin sa inda kuma nan take ya suma kafin daga bisani ya mutu.

Da majiyar mu ta tuntubi jami'an yan sandan jihar jami'in hulda da jama'a ya tabbatar mana da faruwar lamarin inda kuma ya bayyana cewa yanzu haka suna bincike a kai.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.naij.com Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
An fara samun sauki a gidajen man fetur da ke birnin tarayya, Abuja

An fara samun sauki a gidajen man fetur da ke birnin tarayya, Abuja

Layin man fetur da ta kuno kai a Abuja ta fara raguwa sosai a halin yanzu
NAIJ.com
Mailfire view pixel