Zaben 2019: Obasanjo na shirin tsayar da El-rufa'i shugaban kasa

Zaben 2019: Obasanjo na shirin tsayar da El-rufa'i shugaban kasa

Alhaji Abdullahi Sagir, wanda abokin siyasa ne ga tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar, ya na gargadin 'yan arewa akan shirye-shiryen tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo, na yunkurin tsayar da daya daga cikin yaran sa na siyasa na Arewa, a matsayin wanda zai maye gurbin kujerar shugaban Kasa Muhammadu Buhari a zaben 2019.

Sagir ya bayyanawa shafin Daily Trust cewa, tsohon shugaban kasar ya na nan ya tsaya tsayin daka wajen ganin daya daga cikin gwamna Nasir Elrufai ko kuma Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya lashe zaben badi.

A kalamansa; " dole ne mu 'yan Arewa mu hankalata da ire-iren wannan abu, hakan ya faru a baya amma yanzu ba za mu sake bari ba. Ya kamata Obasanjo ya kyale mutane su zabi ra'ayinsu." "Ina dalilin Obasanjo na shirin tsayar da Kwankwaso ko El-Rufai bayan akwai 'yan siyasa managarta da suka fi su?."

Zaben 2019: Obasanjo na shirin tsayar da El-rufa'i shugaban kasa

Zaben 2019: Obasanjo na shirin tsayar da El-rufa'i shugaban kasa

"A shaidawa Obasanjo cewa 'yan Najeriya sun waye yanzu, domin anyi walkiya tun a zaben 2007 kuma komai ya bayyana."

KU KARANTA: Binciken EFCC ya kara nusantawa akan gidajen Diezani na Dubai

A yayin da yake ganawa da manema labaran, Alhaji Abdullahi ya kara da cewa, Atiku zai tsaya takara a 2019, kuma 'yan Najeriya daga kowane yanki sun nuna goyon bayan su a kan hakan.

Ya kuma ce; "sau tari Obasanjo yana fada a cikin magunganunsa na cewar Atiku har ya gama rayuwarsa ba zai shugabanci kasar nan ba. Muna nan cikin roko da addu'a akan ya yi tsawon rai domin ya ga kasancewar Atiku a kujerar shugabancin kasar nan da idanunsa."

Atiku ba ya neman shugabancin kasar nan a wajen Obasanjo, sai dai a wajen Mahaliccin sa, wanda ke bayar da mulki ga wanda yaso, kuma ba tare da sai wani mutum irin Obasanjo ya tsaya ma sa ba."

Domin shawara ko bamu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.naij.com

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://business.facebook.com/pg/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Shin wa ya fi shirga karya, maza ko mata?

Source: Hausa.naija.ng

Related news
An zargi Abba Kyari a kan ajiyar biliyan 50 na NNPC a bankuna wanda ta sabawa tsarin asusun TSA

An zargi Abba Kyari a kan ajiyar biliyan 50 na NNPC a bankuna wanda ta sabawa tsarin asusun TSA

An zargi Abba Kyari a kan ajiyar biliyan 50 na NNPC a bankuna wanda ta sabawa tsarin asusun TSA
NAIJ.com
Mailfire view pixel