El-Rufai bashi da ladabi, bai san girman manya ba - Edwin Clark

El-Rufai bashi da ladabi, bai san girman manya ba - Edwin Clark

- Dattijon yakin kudu maso kudu Edwin Clark yayi gargadi ga gwamna El Rufai

- Dattijon yace gwamnan jihar Kadunan ya dena fadin kalamun battanci ga iyayen kasa

- Daga karshe Clark ya tunatar da El Rufai cewa mulkin da yake takama dashi ba dawwama zaiyi ba

Shugaban kudu maso kudu Chief Edwin Clark ya yi wa gwaman jihar Kaduna Nasir El Rufai kaca-kaca a kan ya ambaci tsaffin shuwagabanni kasa Janaral Yakubu Gawon da Ibrahim Babangida masu karkatar da duk wata dama da ta bayyana a gaban su don ta amfane su wurin ci ma burin su.

Clark ya shaidawa jaridar Vanguard cewan Gawon da Babangida sun isa su haife shi El Rufai kuma ya na sane da manufar garanbaul din da ake ta nanatawa tunda har su jam'iyyar APC sun yi amfani da kalmar lokacin yakin neman zaben su.

El-Rufai bashi da ladabi, bai san girman manya ba - inji Edwin Clark

El-Rufai bashi da ladabi, bai san girman manya ba - inji Edwin Clark

Idan basu aminta da garanbawul din ba kamata yayi su yi ma mutane bayani ba wai su fito suna batanci ga manya kasa ba. A halin yanzun dai mutane sun dawo daga rakiyar APC

DUBA WANNAN: Dandalin Kannywood: Ba duka yan fim mata ke madigo ba - Hauwa Waraka

Su fa tsaffin shuwagabannin kasan babu abinda suke bukata a hannun mutane. Sun dai fadi ra'ayoyin su ne kawai. Haka shima tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar jagora ne na masu neman a yi wa kasa garanbaul. Ya sha nanata a yi wannan garanbawul. Hasali ma ya bada shawaran yin hakan a wata taro na kasa da aka yi a shekarar 2014.

Don mene toh shi El Rufai zai fito ya na batanci ga mutanen da su ka isa su haife shi. Ya kamata ya san matsayin sa.

Na fahimci cewa El-Rufai baya shiri da tsohon shugaban mataimakin kasa Atiku Abubakar domin abinda ya faru tsakanin su amma ya kamata ya sani shi fa gwamna ne kawai kuma wata rana mulkin zata kare.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari,

tuntube mu a labaranhausa@corp.naij.com

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gwarzon ‘Yan wasan kwaikwayo Ali Nuhu na shirin lashe kyautar 2017

Gwarzon ‘Yan wasan kwaikwayo Ali Nuhu na shirin lashe kyautar 2017

Gwarzon ‘Yan wasan kwaikwayo Ali Nuhu na shirin lashe kyautar 2017
NAIJ.com
Mailfire view pixel